A kwanan nan, hankula sun karkata a kan yadda tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai ke ci gaba da ganawa da manyan shugabannin siyasa daga jam’iyyun SDP, PDP da kuma APC mai mulki.
El-Rufai ya gana da dan takarar gwamnan Jihar Sakkwato a zaben 2023 karkashin tutar jam’iyyar SDP, Sanata Abubakar Gada a gidansa da ke Abuja, inda suka yi buda-baki tare.
- Tsananin Zafin Rana Na Janyo Mana Cutar Daji – Shugaban Zabaya Na Kaduna
- Gwamnatin Nasarawa Ta Bukaci Shugaban ALGON Da Ya Daukaka Daarajar Jihar A Idon ‘Yan Nijeriya
Baya ga Gada da el-Rufai, akwai sauran manyan ‘yan siyasa a wannan ganawa da suka hada da shugaban jam’iyyar SDP, Alhaji Shehu Musa Gabam da tsohon dan majalisar dattawa kuma dan takarar gwamna Jihar Oyo a zaben 2023 na jam’iyyar APC, Sanata Teslim Folarin.
Haka kuma ganawar ta hada har da Sanata Nazif Suleiman, jigo a jam’iyyar PDP daga Jihar Bauchi da Hon. Kamel Akinlabi, tsohon dan majalisar wakilai daga Jihar Oyo shi ma jigo ne a PDP da dai sauran manyan ‘yan siyasa.
Wannan ganawa ta wakana ne kasa da sa’o’I 72 bayan da el-Rufai ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar SDP da ke Abuja, inda ya gana da Gabam da sauran jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar.
Bugu da kari, el-Rufa’In ya kuma gana da Sanata Abudul Ningi, wanda Majalisar Dattawa ta dakatar da shi bayan ya yi zargin an yi cushen Naira Triliyan 3 a kasafin 2024.
Idan dai za a iya tunawa, el-Rufai ya bayar da gagarumar gudummawa lokacin yakin neman zaben Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023, sai dai kuma majalisar dattawa ta ki amincewa da shi a matsayin minista sakamakon korafin da ta ce an gabatar mata a kansa.
A irin kwarewa da gogewar siyasarsa, ana ganin yawaitar ganawar da yake yi da ‘yan jam’iyyun adawa na da nasaba da siyasar 2027, kuma ana rade-raden zai iya sauya sheka kamar yadda wata majiya ta bayyana wa LEADERSHIP Hausa.
Majiyar ta ce, “Ko shakka babu haduwar manyan ‘yan siyasan na iya kawo wa Nijeriya sabon fata, musamman a daidai lokacin da mafi yawancin ‘yan kasar nan ke fama da fatara, yunwa, rashin tsaro da dai sauransu.”
Majiyar ta bayyana cewa, Gabam ya siffanta el-Rufai a matsayin abokin da ke da kwarewar siyasa wanda Nijeriya na bukatar shugabanni irin sa.
Majiyar ta kara da cewa Gabam ya yi masa godiya sosai bisa wannan ziyara, inda ya ce a yanzu lokaci ya yi da duk masu ruwa da tsaki a kasar nan za su yi watsi da bambancin kabilanci, yanki da siyasa su rungumi yadda za a ciyar da Nijeriya gaba, musamman a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsaloli da suka hada da yunwa, rashin tsaro, rashin ayyukan yi, garkuwa da mutane, hauhawar farashin kayayyaki da dai sauransu.
Majiyar dai ta boye mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da suka tarbi el-Rufai.
Har ila yau, wasu rahotanni kuma sun bayyana cewa wannan sabon yunkurin na el-Rufai yana da nasaba da ficewa daga jam’iyyar APC, saboda ana ganin an fusata shi a jam’iyyar bisa rashin ba shi mukamin minista.
Sai dai kuma, el-Rufa’I ya musanta shirin sauya shekar domin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. Mai magana da yawun el-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa ko kadan mai gidansa ba ya shirin kalubalantar Tinubu a zaben 2027.
Mashawarcin tsohon gwamnan ya nesanta mai gidan nasa da komawa wata jam’iyya, yana mai cewa cikin sauki mutane ke zunduma karya kan al’amuran da suka shafi siyasa.
Ya ce a matsayinsa na Dan’adam dole ne ya yi cudanya a tsakanin mutane wadanda ba jam’iyyarsu daya ba, sannan dole a tsakanin mutane a samu ziyarar juna da kuma yin tarayya da juna.
Haka kuma el-rufai ya ce a matsayinsa na jigon APC wanda suka kafa wannan gwamnatin, ba zai manta da abokansa ba wadanda ba sa jam’iyya daya.
Ya kara da cewa ya samu damar yin bude-baki tare da abokansa a wannan ziyara kamar irinsu mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribado, wanda shi dan APC ne da Kashim Imam da kuma shugaban jam’iyyar SDP na kasa.
Ko ma dai mene ne, lokaci ne zai tabbatar yayin da kuma ‘Yan Nijeriya suka zuba ido su ga abin da zai wakana nan gaba.