Hasashen yanayi na kwanan nan sun tayar da hankula game da yiwuwar ambaliyar ruwa a Jihar Kano. Hukumar lura da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai yawa a wasu jahohi da suka haɗa da Kano a watannin da ke tafe.
Wannan ƙaruwar ruwan sama, tare da matsalolin magudanun ruwa da gine-gine kan hanyoyin ruwa da Kano ke fuskanta, na ƙara haɗarin ambaliyar ruwa mai tsanani a yankunan birni da karkara. An shawarci mazauna waɗannan yankuna su kasance cikin shiri kuma su ɗauki matakan kariya don tsare rayuka da dukiyoyinsu.
Wani rahoton daga NiMeT ya bayyana cewa za a iya samu ambaliyar daga 16 zuwa 20 ga Yulin da muke ciki a ƙananan hukumomin:
- Abba Ya Sake Nada Tsohon Sarkin Gaya Da Wasu Sabbin Sarakuna A Kano
- Gobara Ta Yi Sanadin Mutuwar Iyalan Kwamishinan Ilimi A Kano
1-Gezawa
2-Gwarzo
3-Karaye
4-Wudil
5-Sumaila
6- Cikin birni
Mahukunta sun fara ɗaukar wasu matakai na shirin rigakafi don rage illar wannan ambaliyar da ake tsammani. Waɗannan matakai sun haɗa da tsaftace magudanun ruwa, da gina katanga ta wucin gadi, da kuma wayar da kan jama’a game da shirin rigakafin ambaliyar ruwa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) tana aiki tare da shugabannin al’umma don tabbatar da cewa mazauna yankunan da ke cikin haɗari suna da cikakken bayani kuma sun shirya don yiwuwar kwashe su. Haka kuma, ƙungiyoyin ba da agajin gaggawa suna cikin shirin ko ta kwana don amsa kiran gaggawa da zarar an samu wani lamari.
Duk da wadannan shirye-shirye, akwai damuwa game da ƙarfin shirin jihar na magance ambaliyar ruwa mai tsanani, musamman idan aka yi la’akari da ƙalubalen da aka fuskanta a baya.
Masana na jan hankalin gwamnati da ta ƙara yin sabon tsarin da zai shigo da ma’aikatar tsara birane da ta kwashe shata da ƙungiyoyin matasa don rage haɗarin na dogon lokaci ba iya damunar bana ba.
An kuma jaddada buƙatar yin cikakken shiri wanda ya haɗa da tsarin gargadi na wuri-wuri kamar a Mota da majalisar Samari da wasu dabarun don gina ƙarfafawa mutane gwuiwa da juriya kan wasu manyan abubuwan da za su iya faru a nan gaba.