Kalaman da Amurka da Birtaniya suka yi ta ofisoshin jakadancinsu da ke nan Nijeriya game da yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a Babban Birnin Tarayya Abuja, sun jefa mazauna birnin har ma da sauran ‘Yan Nijeriya cikin rudani musamman lokacin da Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan lamarin.
Gwamnatin tarayya ta nuna rashin amincewarta a kan rahoton da ofisoshin jakadancin kasashen suka fitar inda Ministan Al’adu da Yada Labarai, Lai Mohammed, yayi watsi da rahoton, a taron da Kungiyar Cibiyar Bunkasa Ilimin Kimiyya Da Al’aduta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta gudanar game da al’amuran yada labarai, a Abuja cikin makon nan.
- Kasar Sin Ta Jinjinawa Hanyoyin Da Kasashen Yankin Manyan Tafkunan Afirka Ke Bi Wajen Magance Matsalolinsu
- Ya Kamata Amurka Ta Soke Takunkumi Idan Tana Son Taimakawa Afirka
Ministan ya nemi kafofin sadarwa a Nijeriya su guji yada labaran da ba a kai ga tantancesu ba musamman ganin irin matsalolin da za su iya haifarwa ga kasa.
Ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya sun fitar da sanarwar cewa, sun samu bayanai na sirri da ke nuna cewa, ‘yan ta’adda na shirin kai hare-haren ta’addanci a wasu cibiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu a yankin Abuja.
A cikin jawabinsa, Minista Lai Mohammed ya ce, gargadi da ofishin jakadancin ya fitar ba yana nuna cikakken halin da kasar nan ke ciki ba ne, kuma wannan sanarwa na iya haifarda rudani a cikin kasa.Ya kuma yi tir da kafafensadarwa masu yada irinwadannan labaran ba tare da sun tantance su ba don dai kawai su cimma wata manufa tasu ba tare da la’akari da halin da ayyukan nasu zai iya jefa kasa ba.
“Wasu kafafen watsa labarai da wasu ‘yan jarida sun shafadawa tafka laifi na yada labarun kanzon kurege saboda kudaden da suke samu tahanyar haka.
“In har ma an bayar da wannan gargadin ne ga ‘yan kasashensu da ke zaune a Nijeriya to me ya sanya takardar sanarwar ta fada wasu kafafen sadarwa wanda hakan ya kai ga tayar da hankulan al’ummar Nijeriya?
“An rufe makarantu, an kulle wuraren kasuwanci, mutane sun dakatar da shirye-shiryen tafiye-tafiyensu amma babu wanda ya damu da tabbatar da sahihancin sanarwar, sun dai buga sun kuma amfana da abin da aka ba su ba tare da damuwada halin da al’umma suka shigaba,’’ in ji shi.Ministan ya kuma kara jaddada matsayarsa ta cewa, Nijeriya ta samu zaman lafiya fiye da yadda al’amarin yake a baya, musammnan saboda sadaukarwa jami’an tsaronmu.
Ya kara da cewa, jajircewar jami’an tsaronmu ya taiamaka wajen samar da tsaro a sassan Nijeriya, kuma a halin yanzu al’amurra sun yi sauki kwarai da gaske a Nijeriya.
A kan haka yabukaci ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu babu wani abin tayar da hankali Mista Lai Mohammed ya kuma bayyana cewa, labaran kanzon kurege na haifar da manyan manyan matsaloli a bangaren tsaro fiye da yadda ake tunani wanda hakan yana barazana ga tabbatuwar zaman lafiya a Nijeriya dama yankin Afrika gaba daya, ya bukaci al’umma su hada hannun don yaki da yaduwar labaran kanzon kurege a Nijeriya A makon jiya ne Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwa da ke bayyana cewa, akwai yiwuwar a kai harin ta’addanci a garin Abuja da kewaye a ‘yan kwanakin nan.
Bayan wannan sanarwa ta yiwuwar kai harin ta’addanci da Amurka ta sanar, sai gashi babban ofishin jakadanci na Birtaniya a Nijeriya ya bayar da sanarwar shawarwari ga ma’aikatanta a kan yadda za su gudanar da zirga-zirgar su a yankin Babbar Birnin Tarayyar Abuja da kewaye, haka kuma wasu ofishin jakadancin kasashen Turai sun sanar da janye wasu muhimman ayyukansu tare da mayar da hankali a kan ayyyukan da suke da matukar muhimmanci kawai.
Amma a wani martani na gaggawa, Hukumar TsaronFarin Kaya (DSS) ta nemi al’umma su kwantar da hankula, tana mai bayanincewa, gwamnati ta dauki matakan da suka kamata don tabbatar da tsaro a yankin babar birnin tarayya Abuja da sauran yankunan Nijeriya gaba daya.
Sanarwa da ta fito daga ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ta bayyana cewa, ‘yan ta’adda sun shirya kai hare-hare gine-ginen gwamnati suna kuma iya kai harin wuraren ibada, kasuwanni, otal-otal, makarantu, filayen wasanni tashoshin mota da ofisoshin jami’an tsaro da kuma ofisoshin kungiyoyin kasashen duniya da ke a birnin Abuja da keweye.
Sanarwa ta bayyana cewa, “Akwai yiwuwar kai harin ta’addanci a Nijeriya musammana Abuja. ‘Yan ta’addan na shirin kai hari wuraren bauta kamar masallatai da coci-coci da ofishosin gwamnati da kungiyouin kasashen waje.
Akan haka ofishin jakadanci na Amurka zai rage ayyukan da yake gudanarwa har sai nangaba, yadda hali ya kasence.”Ofishin jakadancin ya shawarcial’ummar kasar Amurka da kezaune a Nijeriya da su kauracewa wuraren taron jama’a dawurare masu cunkoso, takuma shawarci Amurka wasu kara samar da shiri na musammna don tsaron kansu da iyalansu tare da tabbatarwayar hannunsu na na da caji a koyaushe don ko-ta-kwana.
Shi kwua ofishin jakancin Birtaniya ya bayar da wata takaitacciyar sanarwa ne inda ta bayyana cewa, a ranar Litinin 24 ga watan Oktoba ma’aikata masu gudanar da ayyuka masu muhimmanci ne kawai za a abari su shiga ofishi don gudanar da aiki, an kuma shawarci ma’aikatan su tabbatar da sun nemi izini.
Sanarwa ta kuma shawarci ma’aikatran ofishin jakadancin da kada sukai ‘ya’yansu makatanta ranar Litinin 24 ga watan Oktoba saboda yadda ake da bayanan sirri na yiwuwar kai harin ta’addanci a yankin na Abuja.
Wasu kasashen tarayyar Turai sun dauki wannan ankararwar da matukar muhimmanci suna kuma daukar matakin da suka kamata don kaucewa fadawa matsala.
Bayan fitiowar wannan sanarwar ta kasar Amurka a kan barazanar kai harin ta’addanci a yankin Abuja, makarantu da dama sun dauki matakin kariya inda wata kama ranta ta aika wa iyayen dalibanta wasikar sanarwa kulle makatrantar tare da bayyana fara karatu ta kafar sadarwa ta intanet, sun kuma lura da cewa, suna daukar mataki ne na kariya daga yiwuwar harin ta’addanci da Amurka ta bayar.
Wannan bayani ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu ne a watan Satumba inda aka nuna akwai yiwuwar ‘yan ta’adda su kai hari wasu barikokin sojoji a Nijeriya ciki har da Babban Barikin Sojoji da ke garin Kachia ta Jihar Kaduna, inda bayani ke nuna cewa, a nan ne ake tattare da ajiyar mafi yawan kayan yakin da Nijeriya ta mallaka bayan wadanda suke jibge a Barikin Ikeja ta Jihar Legas.
Rahoton ya nuna cewa, ‘yan ta’addan na shirin samar wa kansu issashen makaman da za su iya mamaye garin Abuja da su ne in bukatar haka ya taso musu. Da manema labarai suka tuntubi wani babban jami’i a Ma’aikatar Kula da Al’ummar Bayanan Sirri na Kasa (Defence Intelligence Agency) a Abuja, ya bayyana cewa, a halin yanzu ana yin dukkan abin da ya kamata don kaucewa duk wani hare-hare da aka ki ya faruwa a yankin Abuja, “kuma jami’an tsaronmu a shirye suke don kawar da duk wata barazana”, in ji shi.
Idan za a iya tunawa a watan Yuli, ‘yan ta’adda sun yi wa tawagar sojoji masu gadin shugaban kasa ‘7 Guards Battalion’ kwantan bau na inda suka kashe akalla Hafsoshi 2 a harin da aka kai musu a yankin karamar hukumar Bwari.
Duk da cewa, sojoji sun gudanar da hari na musamman a yankin inda suka samu nasarar kashe ‘yan ta’adda akalla 30, harin ya tayar da hankali a kanhalin tsaron da yankin na Abuja ke ciki.
Masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaron sun bayyana cewa, harin da aka kai wa rundunar masu gadin shugaban kasar da kuma barazanar da makarantar Lauyoyi da ke Bwauri ta fuskanta a ya musta yanayin zaman lafiyar da yankin Abuja ke samu a ‘yan shekaran nan duk kuwa da matsalar tsaron da ke fuskanta a jihohi makwabta kamar Kaduna da Jihar Neja.
Abin da ya kara tayar da hankula shi ne yadda ‘yan ta’adda suka fasa gidan yarin Kuje Abuja, suka tsirar da mutanesu ba tare da an iya gano shiri da dakile aukuwar harin ba.
A halin yanzu hukumar DSS ta nemi al’umma su kwantar da hankalinsu, don hukumar na daukar dukkan matakan da suka kamata don dakile duk wani shirin aukuwa Abuja.
Bayanin hakan ya fito ne a takardar manema labarai da jami’in watsa labarai na hukumar, Peter Afunanya, yasan ya wa hannu aka kuma raba a Abuja a ranar 23 ga watan Oktoba 22.
“Muna shawartar al’unmma su dauki matakan kariya, ya kuma nemi jami’an tsaro da sauran al’umma su sa da ido tare da bayar da muhimman bayanai da zai taimaka wajen dakile duk wata barazana da zata iya cutar da mu.
“Hukumar DSS na kira daa kwantar hankali don jami’an tsaronmu tare da masu ruwa da tsaki na iya kokarinsu don gani nan tabbatar da zaman lafiya a yankin Abuja da kewaye.”
‘Yansanda Sun Sha Sabuwar Damara
Bayani ya nuna cewa, an tsaurara matakan tsaro a yankin Abuja kasa da awanni 48 da fitar rahoton ofishin jakadancin Amurka. Jami’an tsaro daga rundunar ‘yansandan Nijeriya, Rundunar Sojojin Sama, Sojojin Kasa, jami’an DSS da na NIS sun kara tsaurara matakan tsaro a yankin Abuja.
Wakilinmu ya gano yadda jiragen sama ke shawagi asararin samaniyar Abuja don lura tare da tsara yadda za a tabbatar da tsaro a yankin.
Wani jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, wadannan matakan na zuwa ne bayan umarnin da suka samu daga sama. An kuma lura da kasancewar jami’an tsaro a hanyoyin shiga da fita babbar birnin, an kuma tura sojoji da sauran jami’an tsaro don kula da ma’aikatun gwamnati da manyan kamfanoni masu zaman kansu, masallatai, coci-coci da wuraren shakatawa don tabbatar da tsaron al’umma da dukiyoyinsu.
Mazauna Abuja musamman jami’an ofishoshin jakadancin kasashen waje sun nuna damuwarsu a kan rashin tsaro a yankin musamman bayan hari tare da kubutar da ‘yan ta’adda suka yi gidan yarin Kuje a watan Yuli.
A harin, durarru fiye da 400 suka tsere ciki har da ‘yan ta’adda masu yawa, wanda ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da ayyyukan jami’an leken asiri da suka kasa sunsuno shirin aiwatar da wannan harin A makon jiyan ne Rundunar Soji suka kaddamar da farmakin da suka sanyawa suna ‘Operation Restore Sanity’ inda suka kai samame kasuwannin shanu da ke yankin karamar hukumar Abuja Municipal, a samamen sun samu nasarar cafke wasu ‘yan ta’adda dauke da muggan kwayoyi.
Wani babban jami’in rundunar sojin Nijeriya, Manjo Janar Musa Danmadami, ya kara da cewa, an samu nasarar kama wasu mutum 2 daake zargi da zama ‘yan leken asirin ‘yan ta’adda a kauyen Kwaita da ke karamar hukumar Kwali a yankin Abuja bayan da aka samu bayanai na sirri a kan harkokinsu.
An Tsaurara Tsaro a Ofishoshin Gwamnati Da Ke Garuruwan Yankin Abuja
Wakilinmu ya kuma gano yadda aka tsaurara matakan tsaro a wasu garuruwan da ke kewaye da babban birnin, an kafa shingen binciken motoci ababban ofishin NIS da ke hanyar Dukpa, Gwagwalada, Cibiyar Lissafi ta kasa da ke Sheda, a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja da kuma Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada.
An kuma kafa shingayen bincike na sojoji a Giri kan hanyar Filin Jiragen sama na Abuja, da babbar hanyar Zuba zuwa Kubwa da hanyar Abaji zuwa Abuja zuwa Lokoja.
Da safiyar ranar Litinin an kuma lura da sojoji masu bincike a tashoshin mota na Zuba dana Wazobia da ke Gwagwalada inda suke bincikar kayyakin fasinjoji masu tafiya da masu shigowa garin Abuja, an kuma kafa irin wannan wuraren binciken a wurare da dama don tabbatar da ba a mamayi birnin Abuja da kowanne irin hari a wannan karon, rundunar ‘yansanda ta kaddamar da wani shiri na musamman don dakile shirin ‘yan ta’adda a yankin Abuja, Shugaban Rundunar, Usman Baba, ya sanar da gaggauta kaddamar da shiri na musamman don kawar da‘yan ta’addan wanda da aka yi wa lakabi da “Operation Darkin Gaggawa”.
Ya ce, za a gudanar da shirin ne a shalkwatan ‘yansandan da ke Abuja ranar Talata da Laraba.
A cewarsa, shirin zai kunshi, kawar da zirga-zirgar motoci a wasu hanyoyin cikin birnin da amfani da harsasai mara rai an kuma shirya shi ne don kara zafi da kwarewar jami’an ‘yansanda, ya kuma umarci shugabannin rundunonin ‘yansanda a yankin su tabbatar da jami’an da ke karkashin su suna gudanar da ayyyukansu yadda ya kamata
Matakan Kare Kai Na Haifar Da Da Mai Ido A Yankin Arewa Maso Yamma
Al’ummar wasu jihohin yankin arewa maso yammacin kasar nan sun bayyana cewa, karfafawa al’umma da gwamnati ta yi na mutane su mallaki makamai don kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga yana haifar da dai maiido a halin yanzu.
Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya gudanar ya nuna cewa, mutane sun ji dadin wannan mataki, inda suke cewa, matakin ya taimaka wajen tilastawa ‘yan ta’adda taka tsantsan wajen ayyukansu na cutar da jama’a.
Ya kara da cewa, a halin yanzu ‘yan ta’addan sun fahinci cewa, yakin da ake yi ba a tsakaninsu da jami’an tsaro ne ba kawai don kuwa yanzu mutanen gari mana shiga a fafata da su.
Misali a Jihar Katsina, gwamnatin Jihar ta sanar da cewa, wasu gungun ‘yan ta’adda da dama suna tuntubar gwamnati suna neman a yi sulhu da su don zaman lafiya.
Mataimaki na musamman ga Gwamna Aminu Masari a kan harkar tsaro, Alhaji Ibrahim Ahmed, ya bayyana cewa, ganin babu makawa karshen su yazo, sai suka shiga tuntuba tare da nuna alamun suna neman zaman lafiya da hukuma.
Ya ce, wannan mataki da gwamnati ta dauka wanda ke da nufin karfafa al’umma ya fara nuna alamun nasara musamman ganin yadda hare-haren ya yi karanci kwarai da gaske a halin yanzu.
Ya kuma kara da cewa, za a tabbatar da nasara a kan ‘yan ta’addan ne ta hanyar hada hannu a tsakanin gwamnati da jami’an tsaro da kuma al’umma da kansu.
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta horas da ‘yan kungiyar sa kai na ‘yan banga 1,000 don aikin kare al’umma kuma a shirye suke don kare al’ummarsu daga ‘yan ta’adda, wannan wata alama ce ake aikawa ga ‘yan ta’adda na cewa, lallai al’amarin babu wasa a halin yanzu.
A kan Jihar Sakkwato kuwa, wani masani a harkar tsaro, Skdr. Leader Aminu Bala (mai ritaya), ya lura da cewa, ayyukan ta’addanci ya yi matukar raguwa, sai ya nemi a ci gaba da fafatawa don kawar da su ba tare da kakkautawa ba.
Haka kuma wani mazaunin garin Sabon Birni a Jihar Sakkwato, Laminu Umar, ya tabbatar da cewa, an samu matukar raguwar harkokin ‘yan ta’addaa dan tsakanin nan.
“Ayyukan sojoji a yankinmu ya taimaka wajen kawo karshe harkokin ‘yan ta’adda a yankinmu, an kashe wasu ‘yan ta’addan wasu sun gudu don ba zasu iya fuskantar karfin jami’an tsaronmu ba, don haka ya kamata a ci gaba da fafatawa don kawar da su,” in ji shi.