Wani hatsarin mota mai muni ya yi sanadin mutuwar mutane huɗu tare da jikkata wasu bakwai a kan titin Itobe–Ajaokuta da ke Jihar Kogi. Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Lahadi, inda wata motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 da ke tafiya daga Enugu zuwa Abuja ta yi karo da wata babbar mota da ke tsaye a gefe.
Wani shaidan gani da ido ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudu fiye da ƙima, yana mai zargin direban bas ɗin yana barci saboda gajiya daga doguwar tafiya da dare. Ya ce ƙarfin karon ya nuna alamun rashin kulawa da kuma tafiyar wuce sa’a.
- Ma’aikatan Shari’a Sun Fara Yajin Aiki Kan Bashin Albashi Da Kuɗin Hutu A Kogi,
- Sojoji Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Sace A Dajin Kogi
An tabbatar da cewa gawarwakin waɗanda suka rasu an kai su ɗakin ajiye gawa, yayin da waɗanda suka jikkata ke karɓar magani a wani asibiti a ƙaramar hukumar Ajaokuta.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) a jihar, Tenimu Yusuf Etuku, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’ansa sun isa wajen da hatsarin ya faru, tare da yin alƙawarin fitar da ƙarin bayani daga baya.














