• English
  • Business News
Tuesday, August 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hatsarin Mota Sun Yi Ajalin Mutum 17, 17 Sun Jikkata A Bauchi

by Khalid Idris Doya
2 years ago
in Labarai
0
Hatsarin Mota Sun Yi Ajalin Mutum 17, 17 Sun Jikkata A Bauchi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Akalla mutum 17 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu karin mutane 17 suka jikkata a tagwayen hatsarin mota da suka faru a wurare daban-daban a Bauchi a ranar Litinin.

Mutum sha daya ne suka mutu a hatsari farko, yayin da wasu shida kuma suka rasa rayukansu a hatsarin na biyu.

  • Dan Bindiga Ya Shiga Hannu, Ya Bayyana Yadda Ya Kashe Mutum 15 A Katsina
  • ‘Yan Takaran Gwamna 8 Sun Mara Wa Gwamnan Gombe Baya

Kamar yadda rahoton RS12.11 na ofis din ke kula da Azare zuwa Gamawa na hukumar kiyaye aukuwar hadura (FRSC) reshen jihar Bauchi, hatsarin farko ya faru ne a kauyen Manaba da ke hanyar Zaki zuwa Gamawa da ya shafi mutum 25.

Hatsarin ya ci rayukan mutum 11, manyan Maza 2 da manyan mata 9, sannan wasu 13 kuma suka jikkata Maza manya 3 da mata manya 10.

Hatsarin da ya faru sakamakon fashewar tayar mota kirar Toyota Hummer Mai lamba KTG 13XF ta kabu-kabu da wani direba mai suna Haruna Yusuf ke tukawa.

Labarai Masu Nasaba

Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32

LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya

A cewar rahoton FRSC, hatsarin ya faru ne sakamakon lodin ganganci, gudun wuce kima, fashewar tayar motar da har hakan ya sanya direban ya kasa iya shawo kan motar duk da cewa hanyar titin simul garau yake.

Daga bisani an kwashi wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Gamawa.

Kazalika, hatsarin na biyu da ya ci rayukan mutum shida yayin da wasu hudu suka gamu da munanan raunuka.

A cewar rahoton RS12. 12 na ofishin hukumar kiyaye aukuwar hadura FRSC a Shira da ke jihar Bauchi dauke da sanya hannun DRC, TB Lawal, STO Shira, na cewa hatsarin ya faru ne a hanyar Yana zuwa Giade da ke da tazarar kilomita 10 da cikin kwaryar Yana a karamar hukumar Shira.

Hatsarin da ya hada da motoci biyu na kabu-kabu kirar Volkswagen Golf 2 da suka yi taho mu gama da wata karamar bus din Sharon mai dauke da lamba SHR 203 AA yayin da dayan motar Kuma ba ta da lamba a jikanta da wani mutum Alhaji Bappah Adamu Nasarawa ke tukawa.

A cewar FRSC, Kila hatsarin ya faru ne sakamakon gudun ganganci da ya janyo mutuwar mutum 6, manyan Maza 4 da manyan mata 2 yayin da wasu 10 suka gamu da raunuka daban-daban.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BauchiFRSCHatsarin Mota
ShareTweetSendShare
Previous Post

Mutum 10 Sun Rasu, Da Dama Sun Jikkata A Wani Sabon Hari A Kudancin Kaduna

Next Post

Gobarar Kano: ‘Yan Kasuwar Singa Na Neman Tallafi Daga Gwamnatin Tarayya

Related

Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32
Manyan Labarai

Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32

26 minutes ago
LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya
Labarai

LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya

6 hours ago
Ƴansanda Sun Kama Ƴan Uwa da Wasu Biyu Kan Ƙirkirar Garkuwa Da Kansu A Abuja
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Ƴan Uwa da Wasu Biyu Kan Ƙirkirar Garkuwa Da Kansu A Abuja

7 hours ago
Tsauraran Manufofin Tattalin ArziÆ™in Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – Falana
Labarai

Tsauraran Manufofin Tattalin ArziÆ™in Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – Falana

8 hours ago
BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato
Labarai

BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato

20 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

1 day ago
Next Post
Gobarar Kano: ‘Yan Kasuwar Singa Na Neman Tallafi Daga Gwamnatin Tarayya

Gobarar Kano: 'Yan Kasuwar Singa Na Neman Tallafi Daga Gwamnatin Tarayya

LABARAI MASU NASABA

Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32

Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32

August 5, 2025
Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60

Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60

August 5, 2025
Gwamnatin Yobe Za Ta Yi Taron Girmama ÆŠalibar Turanci Ta Duniya, Nafisa Abdullah

Gwamnatin Yobe Za Ta Yi Taron Girmama ÆŠalibar Turanci Ta Duniya, Nafisa Abdullah

August 5, 2025
Gwamna Aiyedatiwa Ya Bai wa Ƴar Super Falcons Tosin Demehin ₦30m Da Gida

Gwamna Aiyedatiwa Ya Bai wa Ƴar Super Falcons Tosin Demehin ₦30m Da Gida

August 5, 2025
LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya

LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya

August 5, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ƴan Uwa da Wasu Biyu Kan Ƙirkirar Garkuwa Da Kansu A Abuja

Ƴansanda Sun Kama Ƴan Uwa da Wasu Biyu Kan Ƙirkirar Garkuwa Da Kansu A Abuja

August 5, 2025
Tsauraran Manufofin Tattalin ArziÆ™in Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – Falana

Tsauraran Manufofin Tattalin ArziÆ™in Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – Falana

August 5, 2025
BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato

BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato

August 4, 2025
Kasar Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Masu Samar Da Hidimar Intanet

Kasar Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Masu Samar Da Hidimar Intanet

August 4, 2025
Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan Ƙwallon Kwando Ta Mata Da Dala $100,000 Kowace

Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan Ƙwallon Kwando Ta Mata Da Dala $100,000 Kowace

August 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.