Wasu ‘yansanda uku sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
‘Yansandan na tafiya ne zuwa karamar hukumar Giwa bayan halartar bikin Hawan Daushe a birnin Zariya a ranar Lahadi, inda hatsarin ya auku da misalin karfe 9 na dare.
- Majalisar Dokokin Adamawa Ta Tabbatar Da Mace Ta Farko Babban Jojin Jihar
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Biyu Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Adamawa
An ruwaito cewa daya daga cikin tayoyin motar ‘yansanda ne ta fashe a kauyen Sako da ke Kidanda, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar jami’an guda uku.
Wasu uku kuma sun jikkata, inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu a cewar majiyoyi.
Hotuna da aka gani, sun nuna jami’an jina-jina, inda wasu suka samu munanan raunuka a kawunansu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da yi wa jami’an da suka rasu addu’a da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp