Rundunar sojin Isra’ila, IDF ta sanar a ranar Litinin cewa kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta harba rokoki kusan 165 a arewacin Isra’ila.
A cewar ma’aikatar ceto ta Magen David Adom, mutane shida ne suka jikkata, ciki har da wani yaro dan shekara daya, a yankin Karmiel na Galili da kuma yankin Kirjat Ata da ke gabashin Haifa.
- Taron Ƙasashen Musulunci A Saudiya: Tinubu Ya Nemi A Kawo Ƙarshen Ta’addancin Isra’ila A Gaza
- Masanan Afirka Na Dakon Halartar Shugaba Xi Taron Koli Na G20
IDF, ta ce, makaminta mai linzami ya tare wasu daga cikin makamai masu linzami da aka harbo mata, wasu kuma sun fada cikin kasarta.
Kungiyar Hezbollah dai ta dauki alhakin kai hare-hare da dama zuwa yankin Isra’ila.
Tun bayan da aka fara yakin Gaza, sama da shekara guda kenan, mayakan da ke kawance da Iran ke kai hare-hare kan Isra’ila. Isra’ila na mayar da martani da kai hare-hare ta sama da kuma farmaki ta kasa.
Alkaluman da Isra’ila ta fitar, sun ce mutane 74 ne aka kashe a arewacin kasar ta hanyar luguden wuta daga kasar Lebanon tun farkon yakin, wadanda suka hada da fararen hula 43 da sojoji 31, sannan kuma sama da mutane 640 ne suka jikkata.