• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hidimar Yanar Gizo Na Bunkasa Farfadowar Yankunan Karkarar Kasar Sin

by CMG Hausa
3 years ago
Yanar gizo

Saurin fadadar hidimomin yanar gizo ko intanet, a sassan yankunan karkarar kasar Sin, tun bayan babban taron JKS karo na 18 da ya gudana a shekarar 2012, ya ci gaba da bunkasa farfadowar yankunan karkarar kasar.

Cikin shekaru 10 da suka gabata, al’ummun yankunan karkarar kasar, na more hidimar yanar gizo mai sauri da inganci, wadda ke sada su da sauran sassan duniya.

  • Amurka Mai Satar Mai Daga Kasar Sham

Ya zuwa shekarar 2021, fadadar hidimar yanar gizo a sassan karkarar kasar Sin ya kai kaso 57.6 bisa dari, adadin da ya dara na shekarar 2012 da kaso 33.9 bisa dari.

Kaza lika a tsakanin wannan lokaci, adadin iyalai dake kan manyan turakun sadarwa na yanar gizo a kasar ya karu, daga miliyan 40.76 zuwa miliyan 157.7, karin da ya kai na kaso 287 bisa dari. Kari kan hakan, saurin yanar gizo da ake amfani da ita a yankunan karkarar kasar, na yin kunnen doki da na yankunan birane.

A daya hannun kuma, yawan kudaden shiga daga sayayya ta yanar gizo, na kayayyakin da ake sarrafawa a yankunan karkarar kasar ta Sin, shi ma ya karu, daga darajar kudin kasar yuan biliyan 353 a shekarar 2015, zuwa yuan tiriliyan 2.05 a shekarar 2021.

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

A yanzu haka, makarantun firamare da na midil dake sassan kasar Sin, na amfani da intanet mai saurin gaske, inda daliban dake yankunan karkara ke iya cudanya da malamai da sauran daliban dake yankunan birane, tare da daukar darussa ba tare da shiga aji ba.

Bugu da kari, hidimar kiwon lafiya ta hanyar amfani da yanar gizo, ta karade sama da kaso 90 bisa dari na gundumomin kasar Sin, bayan da aka samar da na’urorin dake tallafawa samar da hidimar yanar gizo mai inganci.

Samar da ababen more rayuwa na fasahar sadarwa, na ci gaba da gaggauta rage gibin dake akwai, tsakanin yankunan karkara da na biranen kasar Sin, tare da samar da damar tura sakwanni kai tsaye, da kasuwanci ta yanar gizo, da inganta fasahohin noma, da kiwon lafiya ta yanar gizo, da sauran hidimomin zamani na raya karkara. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
Daga Birnin Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Next Post
Wayar Salula Ta Haddasa Gobara A Gidan Mai A Legas

Wayar Salula Ta Haddasa Gobara A Gidan Mai A Legas

LABARAI MASU NASABA

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.