ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wayar Salula Ta Haddasa Gobara A Gidan Mai A Legas

by Sadiq
4 years ago
Haddasa Gobara

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, ta ce wani mutum ya samu raunuka bayan da wani abu da ake zargin wayar hannu ce ta fashe a wani gidan mai mai zaman kansa da ke garin Badagry na Jihar.

Babban jami’i da ke kula da reshen hukumar na Badagry, Abel Husu, ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) faruwar lamarin.

  • Wani Ya Yi Alkawarin Auren Matashiyar Da Aka Yi Wa Sanadin Rasa Kafa A Sakkwato
  • Allah Ya Yi Wa Hakimin Rimi A Masarautar Katsina NUHU ABDULKADIR Rasuwa

Ya ce hukumar tasu ta samu labarin abin da ke faruwa ne a gidan man Yemoral Oil and Gas Petrol Station da ke kan hanyar Ajara a Badagry da misalin karfe 8:55 safiyar ranar Litinin.

ADVERTISEMENT

Ya ce jami’ansu sun isa gidan man bayan minti 10 da samu rahoton kuma nan take suka fara kokarin kashe gobarar.

“Bincikenmu ya tabbatar cewa wani direban mota ne ya haddasa gobarar, bayan da ya riga ya sayi man fetur a cikin motarsa”.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa

Matashi Ya Yi Ƙaryar Mutuwa Don Gudun Ka Da A Kama Shi Kan Zargin Satar Babur

Ya kuma ce “Bayan da mai motar ya tayar da injin motar sai ta yi bindiga, inda gobara ta tashi nan take”.

Sai dai ma’aikata a gidan man sun shaida wa NAN cewa wani mutum ne ya yi sanadin gobarar bayan da ya amsa wayarsa a daidai lokacin da ake zuba masa fetur cikin wata jarka.

Gidajen mai na saka alamar hana amsa waya a lokacin da ake zuba wa mutum man fetur, wanda watakila hakan na da nasaba da irin wannan lamarin.

MASU ALAKA

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa

November 14, 2026
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu
Manyan Labarai

Matashi Ya Yi Ƙaryar Mutuwa Don Gudun Ka Da A Kama Shi Kan Zargin Satar Babur

November 14, 2026
Gwamnan Bauchi Ya Dakatar Da Sarkin Lame, Duba Dalili
Manyan Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Dakatar Da Sarkin Lame, Duba Dalili

November 14, 2026
Next Post
Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba – Kwankwaso 

Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba - Kwankwaso 

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Wanzar Da Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Wanzar Da Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka

November 14, 2026
Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa

November 14, 2026
Hira Ta Musamman Da Babban Sakataren ASEAN, Kao Kim Hourn

Hira Ta Musamman Da Babban Sakataren ASEAN, Kao Kim Hourn

November 14, 2026
An Kammala Gasar Olympic Ta Dakar Ta 2026

An Kammala Gasar Olympic Ta Dakar Ta 2026

November 14, 2026
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu

Matashi Ya Yi Ƙaryar Mutuwa Don Gudun Ka Da A Kama Shi Kan Zargin Satar Babur

November 14, 2026
Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU ya Buƙaci Ma’aikata Su Rungumi Fasahar AI

Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU ya Buƙaci Ma’aikata Su Rungumi Fasahar AI

November 14, 2026
SAW

Baiwar Da Allah Ya Yi Wa Annabi Muhammad SAW

November 14, 2026
Gwamnan Bauchi Ya Dakatar Da Sarkin Lame, Duba Dalili

Gwamnan Bauchi Ya Dakatar Da Sarkin Lame, Duba Dalili

November 14, 2026
Zainab-Musa-Kwankwaso-and-Governor-Abba

Matar Gwamnan Kano Ta Nemi Saki, Ta Amince Ta Mayar Da Sadakinta

November 14, 2026
APC Ta Kafa Kwamitin Sulhu A Borno

APC Ta Kafa Kwamitin Sulhu A Borno

November 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.