• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi

by Abubakar Abba
5 months ago
Dabbobi

Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi ta Kasa, Idi Mukhtar Maiha, ya yi kira ga matasan kasar nan da su rungumi damar da ke cikin fannin kiwon dabbobi.

Mukhtar, ya alakanta fannin a matsayin mafita kan danyen man fetir, inda ya ce; fannin kiwon dabbobin, na taimakawa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasa.

  • ‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu
  • ‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Na’urorin Zamani Daidai Lokacin Da Sojoji Ke Da Karancin Makamai -Zulum

Ministan, ya kuma kaddamar da tsarin kara habaka kiwon dabbobi na kasar nan daga yawan da yake da shi na dala biliyan 32 zuwa dala biliyan 74, nan da shekarar 2035.

Mukhtar ya alakanta matasa da mata, a matsayin rukunin da za su bayar da gudunmawa, wajen kara bunkasa fannin kiwon kasar.

Ministan ya bayyana haka ne, a jawabinsa na taron matasa da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

Ministan ya kuma zayyano jerin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta kirkiro da nufin zaburar da matasa rungumar kiwon dabbobi, musamman don samun riba ciki har da sama musu hektar noma 51,000, a karkashin hadaka da shirin fitar da kaya na ‘Gulf’ na jihohi da kuma shirye-shiryen farfado da guraren kiwon dabbobi 417 a daukacin fadin kasar nan.

“Muna da abubuwan da za mu yi amfani da su a kasar nan, domin yakar yunwa a fadin kasar baki-daya,” in ji Ministan.

“Akalla a kasar nan, muna da Shanu kimanin miliyan sha biyar da Tumakai miliyan 60 da Kaji da miliyan 600 da Akuyoyi da miliyan 1.4 da Rakuma miliyan 700,000 tare kuma da kasar noma, amma sai dai har yanzu, kasar na shigowa da Madarar Shanu,” in ji shi.

“Wannan wata dama ce, domin abin da muke bukata shi ne, sanya wa matasan kasar karsashin rungumar kiwon dabbobi, domin samun riba,“ in ji Ministan.

Mukhtar ya kuma kalubalanci matasan kasar nan da su yi amfani da fasahar zamani wajen kiwon dabbobin, musamman domin cike gibin noman gargajiyar da ake da shi.

“Ya zame mana wajibi a yanzu a wannan fanni na kimiyya da fasaha, mu kawar da amfani da kayan aikin noma na gargajiya, kamar irin su Fartanya da sauran makamantansu.”

Ministan ya kuma buga misali da shirin ciyar da ‘yan makaranta abinci, wanda ya yi nuni da cewa; idan har za a iya amfani da shirin wajen ciyar da ‘yan makarantar firamare miliyan 47, za a iya shayar da su da Madarar Shanu rabin Lita a kullum, za a iya samun bukatar litar ta Madarar a kasar, za ta karu zuwa sama da miliyan 23, a kullum, wanda hakan zai kuma kara taimakawa wajen samar da ayyukan yi a fannin na samar da Madarar, domin samun riba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci A Sama Wa Manoma Masu Renon Tsirrai Rancen Kudi

LABARAI MASU NASABA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.