A yayin gudanar da ayyukanta na watan Ramadan na kowace shekara, Hisbah ta cafke wasu mutane kan zargin cin abinci a bainar jama’a a gidajen abinci da kasuwanni a lokutan gudanar da azumi.
Kakakin hukumar Hisbah, Lawal Fagge, ya bayyana cewa, sun kama maza goma da mace daya. Inda aka kama yarinyar tana cin abinci a wurin da take sayar da gyada.
- Bai Kamata A Yi Amfani Da Ma’auni Biyu Kan Batun Kare Hakkin Dan Adam Ba
- Ramadan: Sanata Yari Ya Gwangwaje Magidanta 250,000 Da Tallafin Abinci A Zamfara
Ya bayyana cewa, hukumar ta gudanar da ayyukan bincikenta ne a duk fadin birnin, musamman ma kusa da kasuwanni.
Fagge, ya kuma bayyana cewa, wannan dokar ba ta shafi wadanda ba musulmai ba, amma idan sun sayar wa musulmi abinci a lokacin azumi, za a iya ganin hakan ya saba wa doka.
“Mun kama mutane 11 a ranar Talata, ciki har da wata yarinya da ke sayar da gyada.
“Sauran 10 din maza ne, an yi kamen ne a fadin birnin musamman kusa da kasuwannin da ake tafka ta’asa.
“Ba mu kama wadanda ba musulmi ba saboda wannan bai shafe su ba, kuma kawai lokacin da za su iya yin wani laifi shi ne, idan muka gano suna dafa abinci don sayar wa musulmi da ya kamata su yi azumi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp