Hukumar Hisbah a Jihar Jigawa ta kama wasu karuwai 25 a karamar hukumar Kazaure.
Kakakin hukumar ta Hisbah, Muhammad Sale Korau ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa Leadership Hausa.
- Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamnan Jigawa, Saminu Turaki Kan Zargin Almundahanar Biliyan 8.3
- A Watan Nuwamba Za Mu Raba Sabbin Katunan Zaben Da Aka Yi Rijista —INEC
Ya bayyana cewa, kwamandan Hisbah na jihar ya jagoranci samamen tare da samun nasarar cafke mutane talatin da daya a karamar hukumar Kazaure.
Ya ce wadanda aka kama sun hada da, masu mata masu zaman kansu 25 da wasu maza shida bisa zargin sayar da barasa a unguwar Gada a Kazaure.
Rundunar, duk da haka, ta nanata kudurinta na yakar duk wasu munanan dabi’u a jihar.
Ya ce an mika wadanda ake zargin ga ‘yansanda domin gudanar da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp