Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta hana duk wani aiki na gidajen casu a faɗin jihar, tana mai kafa hujja da ƙa’idojin addinin Musulunci da kuma buƙatar kiyaye ɗabi’u masu kyau.
Shugaban hukumar, Dr Aminu Usman (Abu Ammar), ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba a Katsina. Ya ce dole ne masu gidajen casun dare (Kulof) su rufe wuraren domin daƙile ayyukan fasadi, da kare darajar al’umma, da magance matsalolin tsaro a jihar.
- Hisbah Ta Kama Matashi Da Matashiya Kan Yin Aure Saɓanin Dokokin Musulunci A Kano
- Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga
Ya gargadi masu karya wannan doka da cewa za a ɗauki mataki mai tsauri a kansu, inda ya ce an umurci jami’an tsaro da su tabbatar da cikakken bin wannan doka.
“Hukumar ta ƙuduri aniyar gina al’umma mai kyan hali tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Katsina,”
in ji Usman.
Ya kuma tabbatar da cewa an sanar da hukumomin tsaro da suka dace, ciki har da Kwamishinan harkokin tsaro na Jihar, domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni yadda ya kamata.
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,”
in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp