Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ƙara himma wajen rufe wuraren yin caca da ke aiki a unguwannin mazauna Musulmi, bisa la’akari da dokokin addinin Musulunci da ke haramta irin wannan kasuwanci.
Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahid Aminudeen, ya bayyana cewa wannan matakin na zuwa ne sakamakon korafe-korafen shugabannin al’umma da iyaye game da yadda matasa ke tsunduma cikin harkar caca. Ya jaddada cewa hukumar na aiki ne don tabbatar da kiyaye darajar addini da kuma kare matasa daga dabi’un da za su iya cutar da su.
- LGBTQ: Hisbah Ta Yi Bayani Kan Bidiyon Da Aka Ga Jami’inta
- An Gano Dalilin Faruwar Gobarar Kasuwar Kwari A Kano
A yayin wani sumame da aka fara, jami’an Hisbah sun rufe shagunan yin caca guda 30 a cikin wata unguwa. Aminudeen ya ce hukumar za ta ci gaba da wannan aiki don kare matasa da tabbatar da bin ka’idojin addinin Musulunci. Ya ce, “Ba za mu yi ƙasa a guiwa ba wajen rufe ayyukan da ba su da izini tare da ɗaukar matakin doka a kan masu gudanar da su.”
Duk da cewa hukumar Hisbah ta amince da yin caca a wuraren da masu rinjaye Kirista suke, Aminudeen ya bayyana cewa hukumar za ta sa baki ne kawai idan aka samu Musulmai suna zuwa irin waɗannan wurare. Ya kuma bayyana cewa shagunan da dama daga cikin waɗanda aka rufe suna amfani da izinin gudanar da wasannin bidiyo ne amma daga bisani suka mayar da su wuraren yin caca.