Hukumar Hisbah ta jihar Yobe, tare da haɗin gwuiwar NDLEA da NSCDC, ta rufe otal ɗin Maina Lodge tare da kwato ƙwalaben giya 209 a Damaturu, babban birnin jihar.
Shugaban hukumar, Dr. Yahuza Abubakar, ya bayyana cewa an gano motar Golf mai lamba ABJ-144-SC da ke ɗauke da haramtattun kayan a otal ɗin, tare da ƙarin ƙwalabe 34 a ɗakin manyan baƙi (VIP) mai lamba 07.
- Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe
- Hisbah A Katsina Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Wata Budurwa A Wani Faifan Bidiyo
“An rufe otal ɗin na ɗan lokaci yayin da bincike ke gudana don gano direba da wasu da ke da hannu a shigar da haramtattun kayan,” in ji Abubakar.
A wani lamari na daban, hukumar ta rufe wani gida da ake zargin ana aikata baɗala bayan karar da wani mai mai suna Waziri Ibrahim ya yi.
Abubakar ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni da goyon bayansa, yana mai cewa: “Waɗannan nasarori sun nuna jajircewarmu na kiyaye ƙa’idoji da yaƙi da ayyukan haram a jihar Yobe.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp