Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta gargaɗi jama’a kan amfani da wuta a lokacin sanyi, tana cewa wannan lokaci kan haifar da yawan gobara.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ne ya yi wannan gargaɗi cikin wata sanarwa.
- Sin Da Rasha Sun Bukaci A Kare Nasarar Da Aka Samu Daga Yakin Duniya Na II
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Mu’amala Da Taiwan A Hukumance
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya ƙaddamar da yaƙin wayar da kai na wannan shekarar kan illolin gobara a wani taro da aka yi a ranar Laraba.
A taron, Anas ya ce wannan yaƙi yana da nufin faɗakar da jama’a game da haɗarin gobara a lokacin sanyi.
Ya roƙi jama’a su yi taka-tsantsan wajen amfani da wuta musamman a wannan lokaci.
Ya ce ana iya kauce wa gobara idan aka bi ƙananan matakan kariya.
Haka kuma, ya umarci Sashen Hana Gobara ya ƙara wayar da kan jama’a tare da tabbatar da aiwatar da yaƙin a cikin al’umma.














