Hukumar kula ilimin bai daya ta kara bayyana kudurinta na kakkafa dakunan karatu na zamani a kananan makarantu a fadin tarayyar Nijeriya, sai kuma samar da lamarin daya shafi hanyoyin da za a samar da abubuwan da za su bunkasa ilimi ga masu koyo da kuma Malaman makaranta.
Jagoran cibiyar lamarin fasahar zamani na kasa Farfesa Bashir Galadanci, shi ya bayyna hakan lokacin da ya bude taro na uku kan lamarin daya shafi dakin karatu na fasahar zamani, a cibiyar ta UBEC dake Abuja.
Galadanci, shi ne wanda ya wakilci shugaban hukumar UBEC, ya ce dakunan karatu dake amfani da fasahar zamani sun kawo ci gaban, lamurran da suka shafi labarai na fasahar zamani da suka hada da bidiyo, wasanni, da kuma mu’amala tsakanin juna.”
A jawabinta na maraba shugabar sashen al’amuran fasahar zamani, Dokta Hafsat L. Kontagora, ta ce an shirya ita horarwar ne domin a bunkasa da kuma fahimta da gane amfani dakunan karatu masu aiki da fasahar zamani, da kuma samar kwararru masu fasahar shiryawa da yadda za a kirkiri abinda ya shafi labari ko sadarwa ta fasahar zamani.
Ta bayyana cewa taron an shirya shi ne domin a kara bunkasa fasahar hazikana Malaman makarantu da kuma masana fasahar zamani, a kara masu ilimin yadda za su tafiyar da dakunan karatu da yadda za su iya tafiyar da su,domin bunkasa yadda za aga sakamakon koyarwa da kuma gane abubuwan da ake koyawar.
Horarwar ta kwana uku Malaman makaranta ne da manajoji ko jami’an kafar sadarwa ta zamani daga sahun farko na makarantun 13 da suke aiki a Nijeriya wadanda wadansu lamurra na dakunan karatu masu amfani da fasahar zamani, yadda za a tafiyar ko iya gudanar da harkar ilimi,sai kuma irin tunanin da ake yi na irin tafarkin ilimin fasaha zai kasance a gaba.