Hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta karyata rade-raden cewa ta tattauna batun kwace wa Kasar Guinea damar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025.
In ba a manta ba, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF), Amaju Pinnick, ya bayyana a ranar Talata cewa kasarsa (Nijeriya) da makwabciyarta (Jamhuriyar Benin), suna tattaunawa don daukar nauyin gasar cin kofin Afirka ta 2025.
Akwai kuma rahotannin da ke cewa za a iya kwace daukar nauyin gasar ta 2025 daga Guinea saboda yanayin siyasar kasar.
Kasar Guinea dai na karkashin mulkin soji ne tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar da ta gabata, lamarin da ake tunanin zai iya kawo cikas ga shirye-shiryen Gasar a Kasar.
Wani jami’in hukumar ta CAF ya ce hukumarsa ko jami’an kwallon kafa ta Kasar Guinea ba su tattauna batun amsar ragamar karbar bakuncin gasar ba zuwa wata Kasa.