Rundunar Hukumar Kwastam ta Nijeriya(NCS) shiyya ta (FOU B) a ranar 3 ga Agusta, 2025, ta kama wata mota kirar DAF a kan hanyar Yauri-Kontagora a jihar Kebbi.
Motar dai da ake zargin tana dauke da haramtattun kayayyaki da aka boye acikinta, an kawo ta zuwa Kaduna, don tabbatar da kayayyakin dake cikinta inda aka tabbatar tana dauke da buhuna 250 na shinkafar kasar waje.
- Rundunar NSCDC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Hada-hadar Miyagun Kwayoyi A Kano
- Ruftawar Gini Ya Kashe Uwa Da ‘Ya’yanta Biyar A Katsina
Nan take aka kama haramtattun kayayyakin da kudin harajinsu ya kai Naira miliyan 20.51
Kwanturola na shiyyar, Kwanturola AM Alkali, ya yaba wa jami’an bisa yadda suka nuna kwarewa a yayin gudanar da aikinsu.
Kwanturolan ya kuma yabawa muhimmiyar rawar da jama’a ke takawa, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su marawa hukumar kwastam baya a yakin da take yi da zagon kasa ga tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp