Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ta sanar da cewa, kudaden da ta zuba a asusun gwamnatin tarayya ya karu zuwa naira biliyan 501 a shekarar 2023 daga naira biliyan 361 da aka tattara a shekarar 2022.
Shugaban hukumar, Mohammed Bello-Koko, ya sanar da haka a takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Alhamis a Legas, ya ce, an samu wannan nasarar ce saboda sabbin tsare-tsare da hukumar da bijiro da su.
Idan za a iya tunawa kudaden shigan NPA ya karu daga naira biliyan 317 a shekarar 2020 zuwa naira biliyan 361 a shekarar 2022, duk kuwa da zuba kudi ga hadaddiyar asusun gwamnatin tarayya, inda aka zuba naira biliyan 91 a wannan shekarar, a shekarar data gabata an zuba naira biliyan 80.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, a halin yanzu NPA ta kara gudummawarta ga bunkasar tattalin arzikin Nijeriya fiye da kowanne lokaci a baya.
“Aiwatar da sabbin tsare-tsare da kuma aiki tukuru sune suka taimaka mana wajen samun wannan nasarar na karuwar ludaden shiga inda muka samu karuwa daga Naira biliyan 361 a shekarar 2022 zuwa naira biliyan 501 a watan Disamba na shekarar 2023,” in ji shi.
Masu lura da almuran yau da gobe sun yaba wa shugaban NPA Mohammed Bello Koko a kan wannan nasarar, “Tabbas Bello Koko ya bayar da gudummawar da ta kamata’ in ji wani mai sharhi.