Hukumar Kula Da Al’amuran ‘yansanda ta amince da karin girma ga Sufeto 4,741 daga tantancewar da hukumar ta kammala yi wa masu mukamin sufeton ‘yansanda a fadin kasar nan.
Hukumar ta PSC ta kara wa mutane 4,708 girma zuwa mataimakan Sufiritandan ‘yansanda da ba a tabbatar da su ba yayin da 33 suka samu karin girma zuwa manyan sufeto.
Hukumar ta kuma amince da karin girma ga mataimakan Sufeto Janar na ‘yansanda 38 zuwa Sufiritanda da 29 zuwa manyan Sufeto.
A cewar jami’in hulda da jama’a na PSC, Ikechukwu Ani, “Wadannan su ne karin abubuwan da suka faru a cikin cikakken taron hukumar da aka kammala a Abuja ranar Litinin, 21 ga watan Yuli, 2025.
Tun da farko dai hukumar ta yi nazari tare da amincewa da karin girma ga kwamishinonin ‘yansanda 12 zuwa matsayi na gaba na Mataimakan Sufeto-Janar na ‘yansanda, mataimakan kwamishinoni 16 da kwamishinoni 28.
“Sauran su ne Lawan Haruna, Opurum Patrick, Agbo James da Georgewill Onwubiko da sauransu.
“Shugaban PSC ya ce su tuna cewa su abokai ne ga kowa, kuma ya kamata a kowane lokaci su yi daidai da abin da ‘yan Nijeriya ke bukata. Ya kuma ba su tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yin iya kokarinta don ganin an inganta yanayin aikinsu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp