‘Yan sanda sun damke wani mahaifi da ake zargi zai sayar da ‘ya’yansa zabiya guda uku a Mozambique.
An kama mutumin mai shekara 39 tare da kaninsa mai shekara 34, a lardin Tete da ke yammacin kasar a lokacin da suke tsaka da cinikin sayar ‘ya’yan nasa
- Rashin Tsaro: Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula Za Su Yi Addu’o’i Na Musamman A Katsina
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci A Jihar
Kakakin ‘yan sanda Feliciano da Câmara, ya ce bayan su an kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi za su sayi yaran.
Ana kashe zabiya domin amfani da sassan jikinsu wajen tsafi a kasar ta yankin kudancin Afirka.
Kakakin ya kara da cewa yaran uku masu shekara tsakanin 9 da 16, an dauke su ne daga gidansu aka tsare su a wani wuri yayin da cinikin ke gudana.
Cinikin ya haura sama da Dala 39,100 (ko Fam 32,400), in ji mai magana da yawun ‘yan sandan.
Zabiya na fuskantar kalubale a wasu kasashen na Afrika inda ake sayar da su, sannan a kashe wasu don yin tsafi da su.