A kwanan baya ne, Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta ƙasa wato FCCPC da kuma Kotun da ke bai wa masu sayayya kariya, ta tabbatar da cin tarar kamfanin kafar sada zumunta ta Facebook tarar dala miliyan 220 kan yadda ayyukan Kamfanin suka yiwa masu sayayya barazanar a hakkokinsu da kuma yin kuste a sirrisnu.
Ta kuma kara cin Kamfanin wata karin tarar dala 35,000, na kudin da aka kashe wajen gudanar da bincike, inda wannan hakuncin an ya kasance, tamkar wani sako ne mai karfi, aka isar ga manyan Kamfanonin kimiyya da ke yunkurin aikata irin wannan lafin.
Mahimmancin wannan hukuncin na Kotun, ya wuce batun cin Kamfanin na Shugabansa Mark Zuckerberg, amma ya nuna yadda aka kalubalanci, karfin da sauran manyan Kafanoni na duniya suke da shi.
An jima wasu Kamfanonin sadarwa, na yiwa masu amfani da kafar karfa-karfar yin amfani da cikin runbun sirrinsu na adana bayananan su, ba tare da kare hakkinsu ba.
Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38.
A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa.
Wannan Jaridar na da ra’ayin cewa, ‘yayan Kotun uku da Mai Shari’a Alkalan Kotun Thomas Okosun da ya yanke wannan hukunci, sun canci yabo kan tsaywar da suka yi kai da Fata na yanke wannan hukuncin, duk da matsin lambar da suka fuskanta, inda suka tabbatar da ikon da Hukumomin FCCPC da NDPC suke da shi.
Kazalika, abinda ya kara nuna mahimmancin hukuncin Kotun, musamma shi ne, yadda Kotun ta yanke hunci na irin bin ka’idar kundin tsarin mulkin kasa da kuma irin karfin ikon da Hukumar FCCPC take da shi.
Bugu da kari, yin watsi da Kotun ta yi kan jayayyar da Kamfanin na Facebook da kuma son yin zagon kasa kan matakan binciken Hukumar hakan ya nuna cewa, Hukumar za ta iya za ta iya yin amfani da ikonta a kan batun da ya shafi Kamfaninin kasa da kasa.
Hakazailka, Kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa SERAP ta ce, Zuckerberg, ba wai kawai zai biya tarar bane, har da tabbatar da ya yi adalci da kuma biyan wadanda Kamfaninsa, ya yiwa kutse a cikin runbun sirrinsu, duba da cewa, wannan wani bangare ne, na hukuncin da aka yanke.
Wannan batu ne, da ya shafi ‘yancin ‘yan Adam wanda kuma ake da bukatar a tabbatar da anyi adalci.
Za a tabbatar da wannan yanke hukuncin na Koton ne kawai, idan an karfafa shi.
A karkashin sashe na 55 na dokar FCCP, Kamfanin na Facebook, na da ‘yancin daukaka kara kan wannan hukuncin da Kotun ta yanke.
Kazalika, Kotun ta bai wa Kamfanin na Meta, wa’adin kwakuna 60, ya biya tarar da Kotun ta ci shi, wanda sai dai, a bisa tarihin manyan Kamfaninin da kan batun yanke hukuncin Kotu, mai yuwa a samu targanda, wajen biyan tarar.
Idan har Nijeriya ta dauki wannan yanke hukuncin da Kotun ta yi da mahiimanci, dole ne ta shirya karfafa tsarin, wanda hakan zai sanya mai yuwa, sauran manyan Kamfanonin duniya, su bayar da na su hadin kan.
Sarkakiyar da ke cikin wannan Shari’ar, ta nuna yadda ake samun rashin daidaito a bangaren tafiyar da bunkasa tattalin azrki ta hanyar amfani da kimiyyar zamani.
Wannan tarar da dala miliyan 220 ba wata abace da ta taka Kara ta karya ba, idan aka yi la’akari da irin dimbin kudaden shiga da Kamfanin na Meta ke samu.
Misali, zango farko na 2024 Kamfanin ya samu kudin shiga da yawansu ya kai sama da dala biliyan 40.
Wannan jimlar kudin, ya jefa dimbin tambayoyi a zukantan jama’a na cewa, wannan tarar za ta Kamfanin na Meta, za ta dakatar da sauran manyan Kamfanonin duniya, dakatar da nuna halinsa na rashin bibiyayya saboda irin dimbin kudaden shigar da suke samu.
Abinda yake da mahimanci kan cin wannan tarar da Kotun ta yi shi ne yadda Kotun ta nuna cewa, Hukumar ta FCCPC itama ta na da karfin iko, akan manyan Kamfanonin na fasar zamani.
Ya zama wajbi, mu yabawa kokarin Hukumar ta FCCPC, kan mayar da hanhali da ta yi, musamman wajen gudanar da cikaken bincike kan wannan batun.
Kazalika, hukuncin da Kotun ta yanke, abu ne da nuna cewa, kusten da Kmafanin Meta ya yi a cikin rumbun sirrin masu amfani da kafar, abu ne, da ya sabawa dokar kasar nan.
Tun farko, an faro gudanar da wannan binciken ne began in 2020, amma sai 2025 ne, Kotun ta yanke hukunci na karshe.
Wannan yanke hukunci, zai zama tamkar wani darasi, ga sauran kasashen duniya da suma ke ciba da fusknatr irin wannan kalubalen.
Bugu da kari, wannan hukuncin ya kuma tabbatar da ‘yancin da ‘yan Nijeriya suke da shi, kan amfani da kafar sada zumunta ta zamani.
Ba wai kawai biyan tarar ba, dole ne Kamfanin na Meta, ya samar da sauye-sauye kan kare hakkin sirrin masu amfani da kafar da kuma kiyaye dokar kasar nan.
Haka sauran kamfanonin fasaha da ke gudanar da ayyukansu a kasar, dole ne su koyi darasin cewa, yanke wannan hukunci, abu ne da suma ya wajaba su kiyaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp