Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta bayyana rashin amincewarta game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, na tabbatar da zaben Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a jihar.
Tun da farko dai kotun sauraron kararrakin zabe ta ayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Dr. David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
- Gaza: Isra’ila Ta Kashe Mutum 14,200, Daga Ciki Yara 6,000, Mata 4,000 – Jakadan Falasdin
- Kotu Ta Bayar Da Belin Tsohon Shugaban Hukumar KASCO Kan Miliyan 500
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hon. Francis Eokela Orogu, jam’iyyar adawa ta ce duk da cewa tana mutunta bangaren shari’a da bin doka, ta yi imani da cewa hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke bai yi daidai da hujjojin da aka gabatar a yayin zaman kotun ba.
Orogu ya ce, lauyoyin jam’iyyar sun gano wasu muhimman dalilai na daukaka kara wadanda suka yi imanin cewa ya kamata a sake duba hukuncin da kotun ta yanke.
Sanarwar ta kara da cewa: “Jam’iyyarmu za ta shigar da kara a gaban kotun kolin domin neman a yi mata adalci da kuma cikakken nazari kan hukuncin kotun daukaka kara, muna da kwarin gwiwa kan tsarin shari’a kuma muna da kwarin gwiwar cewa za a yi adalci.
Ya kara da cewa “gwagwarmayar tabbatar da adalci abu ne da ke bukatar juriya da hakuri, jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta jajirce wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya da tabbatar da adalci ga al’umma.”