Hukumomi a kasar Sin sun yi kiyasin an yi tafiye-tafiye miliyan 314 yayin hutun ma’aikata da aka yi tsakanin ranar 1 zuwa 5 ga watan Mayu, adadin da ya karu kan na bara da kaso 6.4. Kana adadin kudin da aka kashe wajen yawon bude ido shi ma ya karu, wanda ya kai yuan biliyan 180.3, kwatankwacin dala biliyan 25, karuwar kaso 8 kan na bara.
Mai karatu, shin me hakan ke nufi?
Tabbas a duk inda muka ji karuwar tafiye-tafiye ko kashe kudi tsakanin al’umma, to alama ce ta karfin tattalin arzikin kasa da ma arzikin dake hannun ’yan kasa. Zan iya cewa abun dariya ne idan kasar Sin ta ayyana burin ci gaban tattalin arzikinta na shekara, sannan na ji kafafen yada labarai na kasashen yamma na nuna shakku kan yadda za ta cimma burinta. A iya tsawon zamana a kasar Sin, ban taba jin ta furta wani burin da ta gaza cimmawa ba. Har kullum walwalar al’ummarta da ci gabansu, shi ne babban burin da kasar ta sanya a gaba, kuma a zahiri ake ganin hakan.
Abu na biyu shi ne, kudin da aka kashe a bangaren yawon bude ido shi ma ya karu kan na bara da kaso 8, lamarin dake nuna yadda kasar Sin ke mayar da hankali ga bangaren bude ido musamman wanda ya shafi raya al’adu. Duk wanda ya san kasar Sin, to ya san cewa kasa ce mai matukar mayar da hankali kan rayawa da yayata al’adunta, domin ita ba ta taba sakin al’adunta ta kama na wani ba.
Akwai kuma batun ci gaba da kayayyakin more rayuwa. Hakika tafiye-tafiye ba za su yiwu ba idan babu kyawawan tituna ko layukan dogo ko kyakkyawan tsare tsaren sufuri kamar na jiragen sama da na ruwa da sauransu. Yawaitar tafiye tafiye da aka gani tsakanin al’ummar Sinawa, ya kara haskawa duniya ci gaban kasar Sin da ingantattun ababen more rayuwa dake akwai a kasar.
Sai kuma uwa uba zaman lafiya. Sai da zaman lafiya za a samu kwanciyar hankali har ma a kashe kudi ko a je yawon bude ido da sauran harkoki. Wannan hutu ya kara bayyana cewa, al’ummar kasar Sin suna more zaman lafiya, kuma mabanbantan kabilu a kasar na zaman jituwa da juna.
Hakika kasar Sin ta yi gaba, kuma dogaro da ta yi da karfinta da ma tsara manufofin da suka dace da ita, su ne ginshinkin ci gabanta, wanda babu wani daga waje da zai iya rusawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp