Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kabiru Ibrahim Masari, ya ce a shirye yake a sauya sunansa da wani wanda ya fi shi cancanta idan Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaba Muhammadu Buhari suka ga akwai bukatar haka.
Masari ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da sashen BBC Hausa a Abuja.
Mataimakin Tinubun ya ce ya zuwa yanzu “ta tabbata jam’iyyar APC ta tsaida ‘yan takara Musulmi da Musulmi ke nan a matsayin shugaban kasa da mataimaki”.
Ya ce “Bana tsammanin akwai irin wannan banbancin addini kamar yadda ku ‘yan jarida ku ke zuzuta shi”.
Da yake magana kan zaben shekara ta 2023 kuma, Kabiru Ibrahim Masari, ya ce ba ya tantama APC za ta kayar da babbar jam’iyar adawa ta PDP.
Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da Kabiru Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa na wucin gadi ga hukumar zabe ta kasa (INEC).
Hakan na nufin jam’iyyar da Tinubu za ta shiga neman wanda zai zame mata mataimakin dan takarar shugaban kasa, wanda zai iya taimakawa wajen yakar Atiku da Okowa na PDP.