Masanan kimiyya da bincike-bincike sun gano kaifin basirar da Allah ya yi wa Kurege na rashin mantuwa tare da tsawon tuna yadda ake warware matsala wanda da za a yi amfani da hakan za a samu damar warware sabbin matsaloli wajen gudanar da bincike.
Masana a fanin kimiyya kan binciken da suka gudanar, sun gano cewa, Kurege na da saurin tuna abubuwa da kuma warware matsala da aka shafe kusan shekaru biyu ana neman mafita a kai.
Wani masanin kimiyya da ya yi fice wajen sanin hallayar dabbobi mai suna Dakta Pizza Ka Yee Chow, ya bayyana cewa, hakan ne ya sa Kurge musaman wanda jikinsa ke da ruwan kasa ke jure kowane irin yanayi da ake kiwata shi.
A cewar Pizza, mutane na yin amfani da wasu hanyoyi daban-daban wajen korar Kurege don kar ya yi musu barna, musaman a gonakinsu, amma duk da hakan, Kurege na saurin gano irin wadannan hanyoyin na dabarun manoma.
Shi ma wani masani mai yin bincike kan halayyar dabbobi Dakta Théo Robert ya bayyana cewa, Kurege ba wai kawai yana tuna inda aka ajiye abu ba ne, kana yana kuma iya tuna wasu sabbin dabaru da ba su yi amfani da su da jimawa ba.
A cewar Théo Robert, babu wani bambanci daga abin da muke iya gani ga halayyar dabbobi masu fada domin suna iya tuna wani abu fiye da watanni, musamman a inda suka boye abincinsu.
“Babu wani bambanci daga abin da muke iya gani ga halayyar dabbobi masu fada domin suna iya tuna wani abu fiye da watanni, musamman a inda suka boye abincin su”.
A cewarsa, idan Kurege ya ga wani sabon abu da bai sani ba yakan nuna jin tsoronsa a bayyane, inda yake shafe sama da dakika ashirn kafin ya fara yin wani abu.
Ya kara da cewa, amma suna fara yin wani abu, hakan kan kai shi ‘yar dakika biyu kafin ya tuna, inda kuma zai yi amfani da dabarun da yake da shi tare da koyon wasu kalubalen da ya fusktanta a baya.
Ga nau’ukan Kurege akwai baki da ja da sauran na’uka.
A wata kasida da aka wallafa a cikin littafin halayyar dabbobi, an yi bayani a kan yadda halayyar dabbobi take ciki har da ta Kurege.