Jam’iyyar PDP ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasarta a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, inda ta bayyana cewar jam’iyyar APC da ke mulki ta kassara kasar nan.
Jam’iyyar ta bada tabbacin cewa, dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa, sun shirya tsaf domin shawo kan matsalolin da kasar nan ke fuskanta.
- Ya Shiga Hannu Kan Siyar Wa Mutane Garin Katako Da Siminti A Matsayin Maganin Gargajiya A Kwara
- EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Atoni-Janar Na Legas Bisa Laifin Karkatar Da Kudade
Atiku, wanda ya amshi tutar takarar shugaban kasa daga hannun shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ce kusan kowane fanni a kasar nan ya lalace ga kuma uwa-uba matsalar tsaro da ta addabi kowane dan kasa.
Ya ce a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa a 1999, ta za ma kasa mai bunkasar tattalin arziki da ta fi kowace kasa a Afirika, ingataccen tsaro, samar da ayyukan yi, da sauran abubuwan ci gaba da suka samar, ya bada tabbacin samar da fiye da wadannan muddin aka zabe su a 2023.
“Na rantse, idan aka zabi PDP, matsalar tsaro za ta zama tarihi, za a samar wa matasanmu ayyukan yi, harkokin ilimi za su daidaita,” a cewar Atiku.
Shi kuma a bangarensa abokin takarar Atiku, gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce a shirye suke su hidimta wa kasar nan, kana ya ce PDP tana da kyawawan tsare-tsare na shawo kan tilin matsalolin da suke addabar kasar nan.
“PDP ita ce jam’iyya daya tilo da ta shirya ceto Nijeriya.
Ya kara da cewa, “Atiku gogaggen dan siyasa ne, dan kasuwa ne da zai iya kyautata tattalin arziki da ci gaban kasar nan muddin aka ba shi dama a 2023.”