ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dakarun Soji Sun Kashe ‘Yan Ta’addar ISWAP 19 A Wata Arangama A Borno 

by Sadiq
4 years ago
ISWAP

Akalla ‘yan ta’addar ISWAP 19 ne suka rasa rayukansu a lokacin da dakarun Operation HADIN KAI suka fatattakie su a Gamboru Ngala da ke karamar hukumar Ngala a Jihar Borno. 

Gamboru, wani gari ne mai iyaka da ke nisan kusan kilomita 128 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar.

  • Idan Aka Zabi PDP, Za Mu Kawo Karshen Matsalar Tsaro – Atiku
  • Ya Shiga Hannu Kan Siyar Wa Mutane Garin Katako Da Siminti A Matsayin Maganin Gargajiya A Kwara

LEADERSHIP ta tattaro cewa sojojin tare da wata rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force (CJTF) sun cimma wannan nasara ne a ranar Talata, 11 ga watan Oktoba, 2022 bayan da suka dakile wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’addan suka kai wa sojojin.

ADVERTISEMENT

Wani rahoton leken asirin da Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi ya samu daga manyan majiyoyin soji, wanda wakilinmu ya nakalto, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan da suka zo da adadi mai yawa a kan babura da mota kirar Hilux dauke da bindigu, sun fara kai harin kan sojojin.

Majiyoyin leken asirin sun ce dakarun da ke da karfin gwiwa sun yi musu kwantan bauna wanda ya haifar da kazamin fadan da ya dauki tsawon mintuna 40 ana yi.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Ya ce daga baya sojojin sun mamaye ‘yan ta’addan da karfin wuta wanda hakan ya sa suka tsere.

“Sojojin dai sun fatattaki ‘yan ta’addan da suka koma baya tare da kashe 19 daga cikinsu.

“Sojojin sun yi nasarar kama wata mota dauke da bindigu tasu bayan sun kashe dukkan mutanen da ke cikinta, sun kwato babura tara da kuma makamai da dama da suka hada da PKT daya, AK-47 guda tara da harsashi da dama.

“Ba a samu asarar rai ba a bangaren sojojin saboda biyu ne kawai suka samu rauni a bangarenmu,” in ji wata majiya.

LEADERSHIP ta rawaito cewa sojoji da rundunar hadin gwiwa sun samu nasarar ne biyo bayan bayanan sirri da suka samu a garin Gamborun Ngala.

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Yin Kasuwanci Tare Da Kasar Sin Shi Ne Zabin Karin Kamfanonin Kasashe

Yin Kasuwanci Tare Da Kasar Sin Shi Ne Zabin Karin Kamfanonin Kasashe

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.