Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, Dan Allah idan mace ta yi barin ciki na wata biyu wannan jinin ya zama na ciwo ko za ta daina azumi da sallah?
Wa alaikum assalam. To dan’uwa wannan jini ba zai hana sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa ba ne, malamai suna cewa: duk cikin da ya zube kafin halittar mutum ta bayyana, to ba zai hana sallah da azumi ba, halittar mutum tana bayyana ne daga kwana 80-90 daga samuwar ciki, saboda haka duk cikin ya da ya zube kafin haka, to jininsa, ba zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa ta fara bayyana, to za a bar sallah da azumi.
Allah ne mafi sani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp