A karkashen tattaunawar da marubuciya FATIMA SUNUSI RABI’U ta yi da shafin ADABI, ta bayyana irin nasarorin da ta samu a fannin rubutu, haka nan da kalubalen da abin ya kunsa kamar yadda PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU ta aiko mana kamar haka:
Wanne irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Alhamdu lillah na samu nasarori sosai a silar rubutu, sanin ma mutane nasara ce. Domin silar rubutu na san mutane da dama a jahohi mabanbanta har ma da kasashen ketare ana zumunci da zama na amana. Haka a 2021 na samu nasarar zuwa gwarzuwa ta daya a gasar Tambari Writers an karrama ni kuma an ba ni na kashewa. Haka na samu nasarar zuwa gwarzuwa ta biyu a wata gasa ta Wiwan ita ma an karrama ni. A wannan shekarar kuma ta 2023 labarina ya zamo daya a cikin 13 a gasar Gusau Institute an ba ni Certificate, sannan akwai kananun alkhairai sosai da na cimma nasara duk a silar rubutu.
Me za ki ce da masu karanta littattafanki?
Tsakani na da masu karatu sai sam-barka akwai amana sosai, sai dai na yi musu fatan alkhairi. Kalubale bai wuce na wasu da kake dangantaka da su ba ka ji ana ce maka, baka da aikin yi, rubutu ai wahalar da kai ne, koma a yi maka kallon kamar ba ka san me kake ba. Sauran kalubale kam ba na kallonsu da yazo idan ya wuce nake manta komi.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Kowa yana da buri a rayuwarsa wasu su cika wasu kuma har ka rasu da burinka, ina fatan Allah ya cika mini burikana na alkhairi, wasu daga ciki, ina fatan na yi rubutun da zai zaga ko ina a duniya na shiga cikin wadanda za a dinga kwatance da su kuma yin alfahari da rubutunsu. Sannan ina da burin ganin na bude wata gidauniya domin taimakon marayu da mabukata.
Wanne irin yabo ki ke samu wajen masu karanta labaranki?
Yabawa ta nawa kuwa, gaskiya ina samun mutane da ke yabawa wasu har kira a waya a yaba maka. Bata rai bai wuce na idan kana littafin kudi ba ka dan sami wani akasin da baka yi rubutu ba ka ji ana ta magana musamman ta ‘pribate’ cewa ka amshi kudi amma shuru babu ‘posting’. Wani lokacin dole ne take sa a ji ka shuru kwana biyu, amma kuma da zarar ka ci gaba sai komi ya wuce.
Wanne abu ne idan ki ka tuna shi yake saka ki farin ciki?
Idan na kalli ‘Certificates’ dina wadanda silar rubutu na same su, ina jin dadi sosai.
Bayan rubutu kina sana’a?
Eh! ina sana’a kam, ko ince sana’o’i ma. AlhamduLillah.
Ya ki ke iya hada sana’arki da kuma rubutu?
[Dariya] komai da lokacinsa, sannan gaskiya ni yanzu na tsara yadda nake rubutuna ba kamar baya ba, muna da kungiya ta gwawurtattu uku to mun tsara a duk shekara zamu fitar da labarai guda biyu ne, don haka komai yana da lokacinsa.
Kamar wanne lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
To idan har ina da lokaci kuma ina jin yin rubutun to ina iya yi, kawai dai na fi son yanayin da zan tsince ni shuru babu hayaniya, ina yawan yin rubutu bayan sallar isha’i, dana yi sai na kwanta na yi bacci.
Me za ki ce da masu karanta littafinki?
Ina kaunarsu a kowanne lokaci, kuma ina musu fatan alkhairi sannan ina fatan su ci gaba da bina a duk lokacin da na saki sabon littafi. Ina kaunarsu kamar yadda suke kaunata da littattafaina.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
To ma sha Allahu, ina gaida kanwata Dr Maryamah Ibrahim marubuciya da aminyata Rukayya Ibrahim Lawal sai gawurtattu uku Badi’at Mrs Bukhari da Ummu Maheer Miss Green sannan ina gaishe da Auntyna Hadiza Ibrahim D Auta.