Shaikh Muhajjadina Sani Kano ne Shugaban Kungiyar Masu Ilimin Taurari ta Nahiyar Afrika, a tattaunawarsa da Mataimakin Editanmu Bello Hamza, ya yi bayani dalla-dalla a kan muhimmancin ilimin taurari ga rayuwar al’umma da kuma yadda za a iya cin gajiyar ilimin wajen warware matsalolin da ke fuskantar kasar nan a bangaren tsaro tattalin arziki da zamantakewar al’umma, ga dai yadda hirar ta kasance:
Za mu so ka gabatar da kanka da farko?
Assalamu Alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu. Sunana Shaikh Muhajjadina Sani Kano. Malami ne Ni, masanin ilimin taurari, kuma Majidadin Masarautar Yakanaji.
Ga ka a gidan Jaridar LEADERSHIP Hausa, kuma muna maka maraba. Mene ne ainihin muhimmancin ilimin taurari a cikin al’umma?
Ai muhimmancin ilimin taurari abu ne da yake da muhimmanci, ya fi dukkanin wani abu ma muhimmanci. Sakamakon dukkanin duniyar ma ko rayuwar tana kunshe karkashin ilimin taurari. Wanda ko ka sani ko baka sani ba akansa kake tafe. Akansa kake rayuwa. Akansa kake hawa, ko abin hawa ka hau, akansa kake. Ilimin taurari dai ilimi ne wanda yake gaba daya yake kumshe da rayuwar duniya. Wanda da za a fito a dunga bayyana shi ko kuma al’ummar mu su dawo amfanin da shi da dukkanin wani hargitsi da tashe-tashen hankula da dukkanin wani farin ciki da dukkanin wani alkhairai ta wannan ilimi ake amfani domin a samar da wannan abu.
Ilimin taurari ilimi ne wanda yake gaba daya Allah ya shimfida rayuwar duniya a kansa. Akwai taurarin da suke magana a kan dabbobi, akwai taurarin da suke magana a kan tsirrai, akwai taurarin da suke magana a kan mutane, akwai taurarin da suke yin magana sararin samaniya, akwai taurarin da suke magana a kan kasa, akwai hatta ji, gani, tashi, tsayuwa, dukkanin wani abu da za ka yi akwai tauraron da yake yin magana a kan wannan.
Akramakallah ganin girman muhimmancin wannan ilimi kamar yadda ka yi bayani. Ya lamarin yake kamar a ce ilimin yana da koma baya a cikin al’umma?
Toh, abin da yake faruwa wannan ilimi ga shi ilimi ne wanda dukkanin wani abu da za a yi wannan ilimin ya fi komai muhimmanci, amma kamar yadda ka fada, ya zama koma baya cikin al’umma musamman a nan kasata Nijeriya wanda duk wanda Allah Ubangiji (SWT) ya azurta da wannan ilimi, ba mutum ne wanda za a riga a dauke shi saboda za ka samu a cikin mutane dubu, da wuya ka iya samun masu wannan ilimin guda biyu, uku. Ilimi ne wanda yake da muhimmanci. Ga shi mai wannan ilimin Allah Ubangiji (SWT) ya ba su dama da ilmai na sanin abubuwa iri-iri. Mai ilimin taurari cikin yardar Allah, cikin nufin Allah duk wanda Allah ya azurta da wannan ilimin idan Allah ya yarda zai iya sanin yanzu, me zai faru cikin nufin Allah, gobe, jibi, wannan shekarar, wata shekarar. Cikin ilimin taurari, me ilimin taurari, yanzu misali mu dauka a nan kasarmu Nijeriya, yau mu dauka a kan wannan da ake ta tashe-tashen hankula. Ko kuma yanzu aka dan samu korafe-korafe akan misali matsalar wannan canjin kudi, da za a iya gwamnati za ta iya amfani da mai ilimin taurari ya bada lokaci, da rana da yakamata a ce an sanarwa da al’umma ko an sa dokar ko an waye da za a bi wannan lokacin da wannan sahar da za a yi, ba za a shiga idan Allah ya so ya yarda cikin wannan matsi ba. Kuma ba za a shiga cikin takura ba, sannan abin ba zai zama tashin hankali da damuwa a wasu wurare ba. Har ya nemi ya zama fitina misali.
Sannan me ilimin taurari hatta tashe-tashen hankula da ake samu da waye, misali yanzu idan gwamnati za ta magance abin, idan yau har za ta yi amfani da mai ilimin taurari ta magance matsalar, mai ilimin taurari zai iya sanin ga fa lokacin da yakamata, idan zuwa za a dakatar da masu tayar da tarzoma, idan zuwa za a yi, amma yau ga baki daya saboda rauni na kasarmu, da sakacin kasarmu, yau ga shi an bar masu ilimin taurari. Masu su kuma tada hankula da ake samu musamman a kan Harkar tsaro da ya addabi kasarmu, duk kasar da aka ce babu zaman lafiya dole za ta ga koma baya. Yau misali akan matsalar tsaro; yau sai ga shi suka zo an riga an saki masu wannan ilimi ana ta yin abu a rashin sani, shiyasa gaba daya abubuwa suka riga suka hargitse. Wanda idan za a rika amfani da wannan ilimi ko za a dabbaka masu wannan ilimi gaskiya ina ganin gaba daya duniyarma da za ta zauna lafiya. Wadanda akwai su masu irin wannan ilman duk da dai ba su da yawa cikin al’umma. Wanda yake Allah ne yake zaba. Wanda ka ga a yanzu haka, na samu yanzu matsayin; ina daya daga cikin masu wannan ilimi a Afrika.
Ganin cewa wannan ilimi yana ba masaninsa kamar yadda ka fada sanin abin da zai faru yanzu, abin da zai faru an jima, abin da zai faru gobe ta hanyar ilimi da nazarce-nazarce. Wani tsokaci za ka yi akan masu nuna cewa kamar ana shisshigi ne na sanin gaibu?
A’a! Ai ba sanin gaibu bane ba. Ba kuma ilimi ne na gaibu ba. Saboda idan gaibu ne ko an yi shisshigi yau Allah Ubagiji ya bai wa, yau kamar Likita ko kuma wasu kasashen da suka ci gaba idan za su yi abu, sukan sa wasu kwamfutoci ko wasu Injina ko wasu kayan zamani na kimiyyah, su auna su hango, kuma su fada ta zo ta faru. Kamar yanzu za ka ji ko kafafen watsa labaran sadarwa za ka ji suna cewa insha Allahu gobe za a iya samun ruwa bisa hasashen yanayi da ake yi. Toh hatta su wadannan da suke auna wasu kaya na kimiyya ko kaya na kere-kere abin na su ya leke cikin ilimin taurari. Don da ba ilimin taurari da ba za su samu kwanya da basirar da har za su samu satar amsar da za su kera abubuwan da za su hango ba. Sannan idan ka ce ba mun ce mun san gaibu bane ba, amma ilimin taurari ilimi ne wanda yake zaman kansa. Kuma ko ka yarda ko kar ka yarda rayuwar duniya tana kunshe akan wannan ilimi. Sannan idan ka ce gaibu; mene ne gaibu? Abin da yake gaibu kai dukkanin abin da ba ka sani ba gaibu ne wurinka. Kuma sau nawa ne masu ilimin ake fadar abin kuma a ga ya farun? Wani abin mutum zai zo amma daga ganinsa za ka ba shi labarin kansa gaba daya. Yanzu misali ai ka ga ban san gidanka ba, duk abin da zan fada kan gidanka misali, zan iya kiranshi gaibu ne. Amma kai ka san ba gaibu bane ba. Saboda ka san kana da gidan, kana da mata, kana da yara. To amma idan na zo na fada, duk abin da kai ba ka sani ba, to kai ne yake gaibu a wurinka. To amma abin da mutum yake da yakini akan shi kuma ilimi yana da fadi iri-iri ne. Duk yadda ka zo, idan wani yana fasa ma ilimin da yake da shi sai ka yi mamaki. Saboda haka wannan ba gaibu bane ba. Ilimi ne mai tushe, ilimi ne mai zaman kansa. Amma Ubangiji (SWT) ya kan azurta wasu bayinsa da wannan ilimi wadanda wannan ilimi duk daren dadewa nan gaba idan Allah ya so ya yarda sai duniya ta dawo kanshi. Dama kansa aka yi duniyar, don haka sai an dawo kan wannan ilimi. Ilimi ne mai amfani mai muhimmanci wanda da ana amfani da wannan ilimin da duniyar baki daya ta fi zaman lafiya akan abubuwa.
Yanzu bari mu dan juyo kan abin da ya shafi shugabancin da kake yi na kungiyar masu ilimin taurari na Afrika; ta ya ya ka samu wannan nasarar ganin kai dan Nijeriya ne, dan jihar Kano ne, kuma yanzu ga shi ka tsallake shugabancin tun daga matakin karamar hukuma, jiha, da kasar, yanzu kai ne shugabanta na Afrika?
Alhamdulillahi shi dukkanin wani daukaka, Ubangiji ya kan daukaka bawa a lokacin da ya so, a sanda ya so. Wannan ilimi namu mun taso da shi tun muna yi a anguwa, aka sanmu a kan shi, bangaren dukkannin mutumin da ya riga ya zo mu kan san mene ne matsalar da take jikinshi ba tare da mun sa kwamfuta ba, ba tare da mun auko wani abin awo ba. Amma idan Allah ya so ya yarda dukkanin wani ciwo dake jikin mutum mu kan iya sani, kuma mu kan iya hada mishi magani wanda Allah Ubangiji (SWT) ya ba ni ilimin itace. Duk idan zan shiga daji duk itacen da na gani zan iya gaya ma sunan shi da kuma maganin da yake yi. Wanda duk irin magungunan da za ka je ko a baka ‘tablet’ ko wayeitatuwa ne fa, amma saboda me raunin kasarmu ya sa ba ma iya abin nan. Don haka ta yadda muka riga muka samu wannan abu yau idan wannan ya zo ka taimake shi ya ji dadi, ya gayawa wannan, ya gayawa wannan, kuma idan ka tsarkake zuciyarka, ka yi da ikhlasi, ya zamana don Allah kake riga kake abinka, to Allah zai taimake ka.
Wannan abu ya riga ya samo asali tun muna yi a Anguwa ya fito karamar hukuma, aka zo aka sanmu a jiharmu. Ya zamana jiha-jiha daga ko’ina ana kiranmu, yau har mahukumta suke kiranmu mu ba su shawara akan abubuwa. Daga wannan labari tafi-tafi har ya je har kasashe. Na shiga Chana kan wannan ilimi, na je Jamus, na je Senegal, na je Sudan, na je Turkiyyah, na je Italiya, na je Katar, na je har Saudiyyah a kan wannan ilimi, kuma duk kasar (da na je), gwara ma Saudiyyah na kan yi ibada amma kuma na amfanar da wannan ilimin nawa. Don haka duk kasar da na riga na taka na je, akan wannan ilimi ne. Kuma na samu kyautuka a kasashe daban-daban, na samu kyautuka a kan wannan ilimin nawa.
Akwai lokacin daga Jamus manyan likitoci ne daga kasar Jamus amma suka zo har nan Nijeriya suka zo Kano, masarautar Kano suka karrama ni, suka girmama ni, har suke ma maganar cewa Nijeriya tana da irin wannan mutumin abu ne da na fito musu da shi suka amfane ni ga shi har yau har gobe suna cin gajiyar wannan abun.
Muna godiya
Ni ma na gode.