Babbar illar raba kan mata da wasu Magidanta suke yi ba karama bace wadda kuma take kawo matsalar da zata iya shafar rayuwar duk wadanda suke gidan baki daya.
Domin kuwa matukar shi Maigidan da ya tara dukkan matanda suke gidan bai gyara halin sa na yin abubuwan da basu dace ba, don kawai ya farantawa ita Amaryar zuciyarta,to abin fa daga karshe ba zai haifar da da mai ido ba.
Idanaka yi rashin sa’a har ita Uwragidan ta fita a sanadiyar ko shi Mijin ya sake ta,ko kuma taga cewar ba zata iya jure ma zaman gidan ba, a irin wannan yanayin ta yi tafiyarta.
A karo na farko matsalar da shi Maigidan zai fara fuskanta ko su ‘ya’yanta ita ce ta kula da tarbiyyarsu kamar yadda mahaifiyar su take yi masu,saboda ba dole bane kishoyinta ko kishiyarta su yi ma ‘ya’yan tarbiyyar yadda mahaifiyarsu take yi masu data dace.
Wannan ya nuna ke nan maganar gaskiyar ba ance wasu ba za su iya tarbiyyar ‘ya’yan wasu ba ne,amma abin kallo anan shi ne,wasu da biyu ne da gangan za su yi ta yi masu ingiza mai kantu ruwa suna sa su hanya ko hanyoyin da tarbiyarsu za ta gurbace wanda abin daga karshe su kasa rashin amfanar su kansu da ma masu hulda da su kai tsaye ko a kaikaice.
Shi ma mahaifin ko Maigidan da zai cigaba da aiwatar da irin yara tsanar ko kiyayyar da yake nunuwa nahaifiyar su ‘ya’yan zuwa gare su,duk wani abinda da suka yi ko dai dai ko akasin haka ba zai ce masu uffan ba, sais a masu idanu bama kamar idan aka yi rashin sa’a suna kanana.
Wannan ba karamar illa bace ta kan kuma faru a gidaje daban- daban sa salon halayen Maigida wanda ya kasance mai al’adarnan ta Auri–Saki.
Saboda kuwa tana iya shafar al’ummar gidan gaba daya. Zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kan yi wuya a ire-iren wadannan gidajen, ko Unguwa da ma Gari baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp