Shafin TASKIRA, shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa dabab-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi, neman kudi ta kowacce hanya me kyau ko mara kyau da wasu mutanen ke yi a yanzu, domin biyan bukatunsu na yau da kullum. Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko me za a ce akan hakan?, Me yake janyo hakan, kuma wane illoli hakan yake haifarwa a yanzu?, wane hanyoyi ya kamata abi domin magance irin wannan matsalar?”.
- Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani
- Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Ga dai bayanan nasu kamar haka;
Sunana Princess Fatima Mazadu, Gomben Nijeriya:
To, a gaskiya mafi yawan abin da yake janyo hakan, gasa ne yake haifar da hakan, wani sa’in kuma rashin tuna cewa komai da mutum zai samu ko ya rasa daga ubangiji yake. Mutane suna mantawa da Allah ne ke samar da komai, son ace su wasu ne da kyamatar kansu daga gidan rashi suke duk wannan ma yana haifarwa. Haka ma son zuciya na sakawa mutum ya bi ra’ayin kansa har ta kai ga lalata rayuwarsa don neman kudi. Abubuwan suna da yawa, amma dai wannan kadanne daga ciki.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Gaskiya ba abu ne mai kyau ba, ka nema ta hanyar halal din ma ya aka kare da kudin yanzu, bale kuma ta hanyar haram. Tsabar son abin duniya ne da rashin tsoron Allah, aji tsoron Allah a nemi halal, a nemi kudi ta tsabtatacciyar hanya.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:
Wannan maudu’i ne mai matukar muhimmanci, saboda talauci da son zuciya ya yi wa mutane yawa. Idanun mutane sun rufe, ba sa tunanin ya dace ko bai dace ba. Burinsu kawai shi ne a ina za su samu kudin da za su kashe wutar gabansu, ko kuma su cika burinsu na rayuwa. Lallai kuskure ne babba, a ce mutum ya zama idanunsa sun rufe akan abin duniya, ba ya tsoron Allah akan abin da zai ciyar da iyalinsa. A yayin da mutum ke neman kudi ido rufe, ba ya tunanin lahira ko hakkin wani, ko sakamakon abin da zai same shi, burinsa kawai abin da zai samu. Allah ya sa mu fi karfin zuciyar mu, mu dage da neman halal, mu tsira da mutuncin mu da imanin mu.
Sunana Hauwa Abubakar Sarki:
Lokaci ne da Allah ya kaho mu idan ba kana da shi ba ba za a yi da kai ba. Shi ne dalilin da ya sa wasu mutane suka fada neman kudi ta kowani irin hanya. Abun da za a ce shi ne, mu yi hakuri mu zauna a inda Allah ya aje mu, domin kuwa ba kowa ne Allah ya rubuta yana daga cikin masu arziki ba. Talauci shi ne dalili na farko dake janyo hakan da kuma hangen abun hannun wani, ko nace abun da wani ya samu kai ma kace lallai sai ka samu, wanda hakan ba daidai bane. Mu kasance masu taimako kana mu tsaftace neman mu sai mu ga Allah ya albarkaci abun da zamu samu.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri, A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya rashin yadda da kaddara ce ke jawo haka, domin duk mutumin da ya yadda da kaddara ya san duk wani rabon na dukiya ba zai wuce shi ba don haka ba zai bi hanya mara kyau wajen neman kudi ba. Eh to, dalilan dake jawo hakan suna da yawa, to amma jahilci da rashin tsoron Allah, sune a gaba, domin sune suke jawo haka ga mafi yawan mutane. To hanyoyin dai guda biyu ne, na farko neman ilimin addini domin da shi ne za ka san halak da haramin za kuma ka kiyaye su, sai na biyun tsoron Allah, domin koda kana da ilimi sai kana da tsoron Allah za ka kiyaye halak da haramin.
Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:
Taulauci da rashin aikin yi, ga tsadar rayuwa da kullum take karuwa, nauyi na yi wa al’umma yawa suna rasa mafita a rayuwarsu, shi yake haifar da hakan. Wasu kuma son zuciya ne. Kowa ya rika tuna cewa akwai mutuwa, wanda ya yi daidai ya sani, haka ma wanda bai yi ba ya sani.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:
Neman kudi ya dace, amma ta hanyar halal. Abin da yake kawo hakan talauci da aka jefa al’ummar wannan kasar. Babbar hanyar ita ce, mu ji tsoron Allah muna tuna cewa bawa ba zai taba wuce rabonsa ba. Shawarata a nan ita ce mu tuna cewa babu bawan da zai koma ga ubangijinsa ba tare da ya bar daidai da kwayar zarra na arzikinsa ba, don haka mu tsaya mu nemi halal dinmu domin mu zauna lafiya. Allah ya sa mu dace amin.
Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:
Gaskiya wasu talauce ne, wasu kuma san abu duniya ne ya yi masu yawa, shi ya sa suke neman kudi ta kowace hanya. Ni na ga wata da idona wanda har sai da nasa baki, amma na ga ta yi nisa ba ta jin kira. Wai za ta kasar waje neman kudi, babu inda ya fi gida dadi. Shawara ta a nan shi ne, in zamu nemi kudi mu neme shi ta hanya mai kyau, kuma mu kula. Allah ya ba mu dace wa.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori:
A yau, yawaitar matsin rayuwa da kalubalen yau da kullum ya sa mutane da dama ke neman kudi ba tare da la’akari da halal ko haram ba. Wani zai nemi hanyar kirki ya samu na halak, amma wasu kuma za su zabi hanyar da ba ta dace ba kamar sata, damfara, ko karuwanci, duka da nufin biyan bukatunsu na yau da kullum. Wannan hali yana da illa ga dabi’a, addini da tsaron al’umma. Idan kowa zai nemi kudi ta kowacce hanya, to rayuwar al’umma za ta zama barazana, domin ba za a samu gaskiya, aminci da mutunci ba. Mu fahimci cewa arziki na gaskiya yana zuwa ne da hakuri, tawakkali, da bin hanyoyi na gaskiya da halal. Duniya ba za ta kare da wahala ba, amma samun riba ta haram tana da sakamako mai muni a nan duniya da lahira.
Sunana Hussy Saniey, daga Katsina:
Rashin tawakkali shi ne linzamin da ke kai wasu mutanen ga aikata haka. Ya kamata a kodayaushe mutane su rika jin tsoron Allah tare da tunawa yana kallonsu a duk wani motsinsu, don haka su kiyaye jikinsu daga haram, domin duk jikin da aka gina da haram ba ya shiga aljanna. Mutane su jajirce a wurin neman halal, duk wanda ya tashi ya nema Allah zai sanya ma shi albarka a cikin neman, a guji cin dukiyar da ba ta da tsarki.
Sunana Nura Garba, Tsanyawa, A Jihar Kano:
Yana da alaka da sauyin zamani da al’umma suke son yin kitsan wance amma basu da gashin wance, ga kuma tarun bukatu marasa manufa, da yanzu sai ka ga mutum yana neman kudi ta kowace hanya don kawai ya sai mota irin ta wani. Abin da yake kawo haka shi ne, rayuwar karya da yin gasa da wasu ke yi, sai rashin godiya ta rufin asiri da cikakkiyar lafiyar da Allah ya bawa dan’adam. Hanyoyin magance hakan yadda da samu da rashin na Allah ne, kuma kowa rabonsa zai ci kafin ya bar duniya, don haka ya kamata al’umma su nemi halak ta halastacciyar hanya.














