Yadda Allah (SWT) ya halicci Dan Adam, kaso 60 cikin 100 na jikin namiji ruwa ne zalla, inda mata kuma kaso 55 na jikinsu su ma ruwa.
Don haka, wannan yana nuna cewa fiye da rabin jikin Dan Adam ruwa ne, saboda haka da zarar an ce babu wannan ruwan tare da mu, kenan babu rai kwata-kwata.
- Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kama Hanyar Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba A Yankin Tsaunin Himalaya
- Manyan Ayyukan Da Ke Gaban Sabon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya
Har ila yau, shan ruwa na da matukar amfani a tare da mutane, domin kuwa a kullum ruwa na fita daga jikinmu, idan muka je yin fitsari ko bayan gida ko yin zufa, kai har ma yayin da muke yin numfashi.
Kazalika, ana bukatar da namiji ya sha ruwa kimanin lita 3.7, mata kuma su sha lita 2.7 a kowace rana. A nan ana auna yawan ruwan da mutum ke sha ne wanda ya hada da shayi ko lemo ko kuma jus.
Idan kuma zallan ruwan mutum zai sha kamar ‘Pure Water’, namiji ana so ya sha kamar guda bakwai da rabi, mace kuma ta sha guda biyar da rabi.
Amma a nan ana magana ne a kan lafiyayyu, wadanda ba su da cikakkiyar lafiya kamar masu ciwon zuciya ko koda, bai kamata su sha wannan adadi ba.
Rashin yawan shan ruwa yadda ya kamata zai iya jawo wa mutum illoli daban daban. Na farko, rashin shan ruwa akai-akai zai iya haddasa wa mutum ya kamu da cutar sanyin fitsari (Urinary track infection).
Na biyu kuma, zai iya haddasa wa mutum cutar tsakuwar koda (Kidney stones), a nan wasu abubuwa ne ke dunkulewa su ki fita su zama kamar dutse, wanda hakan ke sa wa mutum ya rika yin ciwon ciki mai zafi tare da yin fitsarin jini da sauran wasu matsaloli da dama.
Na uku kuma, rashin yawan shan ruwa na iya janyo rashin iya yin bayan gida, wanda hakan kan kawo matsalar basir da sauran makamantansu sakamakon sakaci da yawan shan ruwa.
Don haka, ya zama wajibi mu kula da shan shan ruwa yadda ya kamata, domin kaucewa haduwa da ire-iren wadannan cututtuka, kamar yadda a koda-yaushe likitoci ke kokarin fadakarwa tare da jan hankalinmu.