Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa yana da ƙwarewa da abin da ake buƙata don zama shugaban ƙasar Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
- Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
- UEFA: Barcelona Ta Kai Zagayen Kusa Da Karshe A Karon Farko Cikin Shekaru 9
Makinde, wanda ke wa’adin mulkinsa na biyu a jam’iyyar PDP, ya ce yana da cikakken ikon shugabantar ƙasar, amma hakan zai dogara ne da abin da ‘yan Nijeriya da jam’iyyarsa ke so.
“Ina da tabbacin cewa ina da ƙwarewar zama shugaban ƙasa. Amma shin hakan ne ‘yan Nijeriya ke so a yanzu? Shin jam’iyyata za ta goyi baya? Har yanzu lokaci na nan,” in ji shi.
Makinde ya kuma ce zaɓen 2027 zai fi shafar zaɓin ‘yan Nijeriya fiye da yaƙi tsakanin jam’iyyar PDP da jam’iyyar APC mai mulki.
Ya jaddada cewa dole ne a gyara jam’iyyar PDP kafin a fara tunanin neman wani muƙami.
Ya ƙara da cewa ko da siyasarsa ta tsaya a matsayin gwamna, zai kasance cikin farin ciki da gamsuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp