Mai tsaron ragar Manchester United ,André Onana na da niyyar ci gaba da zama a Manchester United duk da tayin da ya samu daga kungiyoyi daga kasar Saudi Arabiya, kasancewarsa zabin koci Rubin Amorim a ragar Kungiyar tun bayan zuwanshi a watan Janairu.
Ana danganta Onana da komawa kasar Saudiya a bazara mai zuwa domin buga gasar Saudi Pro League ta kasar idan ya bar Old Trafford, ganin cewa, babban kocin United Ruben Amorim na neman sake fasalin kungiyar gabanin kammala kakar wasa ta bana.
- Karin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arzikin Duniya
- Karfin Lantarki Da Tashoshi Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Ke Samarwa A Sin Ya Kai Kilowatt Biliyan 2
Majiyar ESPN ta bayyana cewa, Onana ya na son ya ci gaba da zama a Old Trafford, Onana mai shekaru 28, ya na da kwantiragi har zuwa shekarar 2028 tun bayan da ya zo daga Inter Milan a kan yuro miliyan 43 a shekarar 2023, wata majiya ta shaida wa ESPN cewa United na tunanin sayen mai tsaron raga a lokacin bazara.
Tom Heaton da Altay Bayindir ba su samu lokacin da suke bukata a United ba, Bayindir ya buga kananan wasanni a kakar wasa ta bana, amma kuma tsohon mai tsaron ragar na Fenerbahce na fatan ganin ya samu karin lokacin buga wasanni kamar sauran yan wasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp