Biyo bayan hukuncin kotun kolin Nijeriya kan karar da ‘yar takarar gwamnan jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani ta daukaka, mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa G. Farauta, ta bukaci Binani da ta goyi bayan gwamna Ahmadu Umaru Finitri.
Farauta, ta kuma gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’in samun nasarar da suka rika yi wa gwamnatin bisa imanin da karfin gwiwar da suke dashi a kanta.
- Nijeriya Ta Yi Allah-Wadai Da Ficewar Nijar, Mali Da Burkina Faso Daga ECOWAS
- Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri
Ta ce “Yanzu duk shari’a ta kare, za a kara ganin yadda ake gudanar da mulki, za a mayar da hankali ga samar da ingantacciyar gwamnati a Adamawa” in ji Farauta.
Mataimakiyar gwamnan, wacce ke magana a gidan gwamnatin jihar tare da kakakin majalisar dokokin jihar, da sauran mukaraban gwamnati, ta gode wa bangaren shari’a, ta kuma jaddada bukatar samun hadin kai da goyon bayan jama’ar jihar domin ciyar da jihar gaba.
“Ina kira ga al’ummar Adamawa da su hada kai da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, bisa kudurinsa na ganin jihar ta samu zaman lafiya da ci gaba ta hanyar tsarin gwamnati na jama’a.
“Jama’ar Adamawa iyali guda ne, jiharmu ce baki daya, mu kyale batun jam’iyyarmu, Addini da bambancin kabilanci domin samun ci gaban jiharmu.”
Da ta ke magana kan zaman kotun na ranar Laraba, ta ce “Dama Aishatu Binani ta jam’iyyar APC, ta garzaya kotun kan zaben gwamnan 2023, ta bukaci kotu ta tabbatar da hukuncin da dakataccen kwamishinan zaben hukumar zaben jihar Hudu Yunusa Ari, ya bayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
“Kotun Koli mai mutum biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro, ta amince da hukuncin da kananan kotunan baya suka yanke, inda suka bayyana abin da kwamishinan zabe Hudu Ari ya yi a matsayin mummunan aiki.
“Kotun kolin ta lura da cewa batun shi ne, na wanda ya lashe zabe da mafi yawan kuri’u, na gaskiya, kuma babu wani abu a gaban kotun daukaka kara da ke nuna cewa wanda ake kara na biyu (gwamna Fintiri), bai samu kuri’u mafi rinjaye na gaskiya ba.
“Don haka ta amince da hukuncin kotun daukaka kara, saboda haka ta yi watsi da karar” in ji Farauta.