Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II ya bayyanawa shugabannin tsaro a ganawar da suka yi a jiya Asabar cewa, har yanzu bai ga wata kotu da ta hana a maido da shi a matsayin Sarkin Kano ba.
Ya bayyana cewa bai ga takamaiman umarnin kotu ba, kawai a labarai yake jin wai kotu ta bayar da umurni.
Sarkin wanda ya yi magana na sama da sa’a guda yayin ganawarsa da shugabannin tsaro, ya shaida cewa, abin da gwamnatin jihar ta yi shi ne adalci kan rashin adalcin da aka yi masa a baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp