• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ina Nan Kan Bakana Ban Yarda Malami Ya Shiga Siyasa Ba, Amma… – Farfesa Makari

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
Malami

Babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya bayyana cewa yana nan kan ra’ayinsa bai yarda malami ya shiga siyasa ba, amma yana so a bambanta abubuwa guda biyu.

“Bana sha’awar malami ya shiga siyasa daban, amma idan ya kasance wannan malamin yana da wasu ilimi na rayuwa wanda ya shahara a kai, idan har ya shiga siyasa to ko ya yi kuskure ba za a danganta wannan kuskuren da addini ba. Abin da ake nufi dai ilimi ne kadai abin da ake bukata.”

  • Zan Bayyana Dan Takarar Da Zan Mara Wa Baya A Janairu – Wike
  • An Kammala Kashin Farko Na Layin Dogon Jihar Lagos

Farfesa Makari ya kara da cewa akwai hakkin shugaba a kan talakawa, haka kuma akwai hakkin talakawa a kan shugaba wanda suka hada da biyyaya da kuma adalci.

Ya ce wannan zabe da za a gudanar shaida ce da Allah zai taimaya a kai ranar Lahira. Ya ce duk wanda ka zaba kar ka dauka abin wasa, kamar yadda ake raba wa mutane kudi ko omo domin su zabi mutum. A cewarsa, wannan kudi ko omo da aka ba ka domin yin zabe, ka tabbatar da cewa shaida ce wanda Allah zai tambaye ka a ranar tashin kiya.

Farfasa Makari ya shawarci mutane su duba wadanda suka fi yi musu zaton alkairi kamar yin adalci, tausaya wa al’umma, to ka gina zabenka a kan wannan turbali na zaben shugaba. Ya ce lallai mutane su duba wanda zai fi yi wa al’umma abubuwan da suka kamata a zaben shugaba domin su, sai ka yi kokarin gina zabenka a kan wannan ma’auni, amma duk lokacin da al’umma suka makantar da idanuwansu da hankulansu suka gina zabensu kan yadda mutane ke dibar miliyoyin kudade suna wazawa domin a zabesu har su hau wasu mukamai a kan su magance matsaloli, to lallai ba a shirya ganin lokacin magance matsalilin ba.

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

Ya ce ba zai taba iya fahimtar kishin kasa da za ta sa mutum ya dunga kwaso kudi yana kokarin sayan kujerar da zai yi wa al’umma aiki a kanta ba.

“Ni dai a fahimtata na kasa gane wannan kishin kasa wanda mutum zai kwaso kudi yana rabawa domin ya sayi kujerar da zai yi wa al’umma aiki a kanta.”

Farfasa Makari ya ce, “Akwai kalubale mai girma a gabanmu, abun da ake fadi na cewa ko ka zaba ko baka zaba ba za a zaben maka, wannan magana ba gaskiya ba ce. Lallai wanda zai shugabanci al’umma, yanke hukunci na karshe yana hannun al’umma ne wanda suka bi layi domin zaban wanda zai shugabance su.

“Kaurace wa zabe, mutum ya ce ba zai yi zabe ba saboda wasu dalilai, to zai iya zama kara taimakon masu barna a kan barnar. Saboda ko ka yi zabe ko ba ka yi ba a ranar da za a rantsar da shugaba dole ne a rantsar da shi. Domin rashin zaben ka ba zai sa a kasa rantar da wanda za a rantsar ba.

“Saboda haka, ‘yan’uwa mu yi kokari mu zabi cancanta. Ka da mu mayar da kanmu koma-bayan da wani ya ce mana ku zabi wane, domin muna da hankular kanmu. Sannan kar mu gina zabenmu a kan jam’iyya, dama a farkon maganana na fadi cewa damokuradiyyar nan iya kokarinta take yi ta yi abin da yake daidai, amma karka dauka komi nata daidai ne.

“Idan mutum ya ce maka jam’iyya kaza za ka zaba daga sama har kasa domin ra’ayinsa wanda ba ita ce daidai ba, kai kuma ka duba cancata. Ya kamata mu gane babu wata jam’iyya a yanzu, domin ‘yan takara nawa ne suka sauya sheka wanda har wurin kamfen suna kuskuran iya fadin jam’iyyarsu, saboda sabawa wanda ya kasance jiya suke can, yanzu kuma suna nan, wanda hakan ne ya sa suke kuskuren fadin sunan jam’iyyunsu.

“Bai kamata ana ci gaba da yawo da hankalinmu ba, ya kamata mu yi kokarin gina zabenmu a kan wadanda suka cancanta,” in ji Farfasa Makari.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Next Post
“Ba Zamu Raba Wa Mata Da Matasa Akuyoyi Da Sunan Tallafin Sana’a Ba A Bauchi” —Sadique

“Ba Zamu Raba Wa Mata Da Matasa Akuyoyi Da Sunan Tallafin Sana'a Ba A Bauchi" —Sadique

LABARAI MASU NASABA

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.