Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki gafarar ‘yan Nijeriya yayin da yake kokarin yin bankwana da mulki.
Ya yi wannan roko ne a wajen bikin Sallah karo na tara kuma na karshe da mazauna babban birnin tarayya karkashin jagorancin minista Mohammed Bello, a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa, a Abuja.
- Fadar Shugaban Kasa Ta Kare Buhari Kan Ayyukan Da Ya Yi A Mulkinsa
- Yadda Uwargida Za Ta Yi Kwalliyar Gida Da Sallah
Shugaban ya kuma gode wa ‘yan Nijeriya da suka yi masa uzuri cikin shekaru bakwai da rabi na gwamnatinsa.
“Ina ganin wannan abu ne mai kyau a gare ni na yi bankwana da ku kuma ina gode muku da kuka min uzuri fiye da shekaru bakwai da rabi zuwa yanzu.”
“Ina tabbatar muku zan yi kewae soyayyar da kuka nuna min, don ina ganin na samu damar da zan roke ku ku yafe min.
“Da yake na zama Gwamna, Minista da Shugaban kasa sau biyu, ina ganin Allah ya ba mu dama ta zama shugabanku. Kuma na gode wa Allah a kan haka. Don haka, don Allah duk wanda ya ji na yi masa ba daidai ba, mu duka mutane ne. Babu shakka na cutar da wasu kuma ina fatan za ku gafarta mini. Kuma wadanda suke ganin na cutar da su don Allah ku gafarta min.”