ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fadar Shugaban Kasa Ta Kare Buhari Kan Ayyukan Da Ya Yi A Mulkinsa

by Idris Aliyu Daudawa
3 years ago
Buhari

Yayin daya rage kwana ma gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu kwana 43 ta kammala wa’adinta na biyu abinda ya kai shekara takwas ke nan,fadar Shugaban kasa ta cigaba da kare shi inda take jinjina ma shi kan  ayyukan cigaban da yayi.

Mai ba Shugaban kasa shawara na musamman akan yada labarai da wayar da kan al’umma Femi Adesina,ya ce Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a mulkinsa wajen tunkarar matsalolin da suka shafi tabarbarewar tsaro.

  • Tattalin Arzikin Sin Ya Kara Samar Da Dama Ga Bunkasuwar Sauran Kasashen Duniya
  • Bangaren Sin: Ya kamata Al’ummar Kasa Da Kasa Ta Goyi Bayan Kasashen Yankin Manyan Tabkuna Wajen Gina Makomar Bai Daya

Ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Nijeriya fiye da yadda ya same ta a lokacin daya amshi kambun mulki a watan Mayu shekarar 2015.

ADVERTISEMENT

Adesina tsohon babban Editan Jaridar Sun wanda aka nada shi a matsayin mai magana da yawun Shugaban kasa a watan Mayu na 2015 lokacin da Buhari ya hau kan karagar mulki watan Mayu 2015, an sake nada shi kan mukamin a karo na biyu watan Agusta 2019 bayan an sake zaben Buhari a wa’adinsa na biyu.

Da ake hira da shi a shirin gidan Talbijin na Channels mai taken ‘Suyasa Ayau’,Adesina ya ce babban aikin da maigidan shi ya yi ba wani shakku dangane da hakan.

LABARAI MASU NASABA

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

“A shekarar 2015 kowa ya san inda Nijeriya take domin akwai kananan hukumomi 17 da suke karkashin ‘yan ta’adda kamar yadda ya bayyana”.

Da aka tambaye shi ko an samu wani cigaba sai ya ce,“da akwai ci gaba.Yawansu na raguwa sannu a hankali a shekaraun da suka gabata yanzu abin ya zama tarihi babu wani wanda zai canza al’amarin”.

Bugu da kari yayi karin bayani kan nada mukaman Shugabannin rundunonin tsaro wanda kamar yadda yace abin ba abin tafarkin samun daidaituwa,ko kuma al’ amari mai nasaba da kabilanci ko yin abinda ya dace.Shugaban kasa Buhari yana da dama ya nada wadanda yake ganin za su iya aikin na kwato Nijeriya daga hannun ‘yan ta’adda.

“Kar ku hada al’amarin tsaro da kabilanci kada ku hada shi da sai an biya hakkin kowa,maganar gaskiya yana da damar ya nada duk wanda yaga ya dace mukami.Maganar gaskiya tsarin mulkin da yayi magana kan ayi abu ba tare da wata mina- mina ba shi yaba Shugaban kasa dama ta cewa yana iya ba duk wanda yaso mukami”.

Buhari da yake daga Jihar Katsina yake sashen Arewa maso yamma ana ganin laifinsa domin yadda ya fifita ‘yan Arewa a wurin bada mukamai.Watan Nuwamba na shekarar data gabata lokacin da ake kamfen na zabubbukan 2023, dantakarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar,ya ga laifin Shugaban kasa Buhari kan abinda ya kira da sauran aiki na yadda ya bada mukaman Shugabannin rundunonin tsaro,ya ce masu jagorancin hukumomin da suka shafi tsaro daga Arewa su ke.

Ko da aka nuna masa alkalumma da ba na kunbiya- kunbiya ba da ke nuna tsakanin watan Mayu 2015 da Mayu na 2022, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane,’yan bindiga dadi sun kashe ‘yan Nijeriya fiye  da 55,000.Adesina ya dage ne da cewa Shugaban kasa zai bar halin tsaro cikin sauki fiye da yadda ya samu al’amarin ba a cewa komai a shekarar 2015.Yana cewa lokacin da Buhari ya fara mulki akwai ‘yan ta’adda da suka mamaye fadar wasu Sarakuna a wasu sassa na Arewa.

Kamar yadda ya jaddada, “Abinda nake nufi da su suke kulawa da fadar Sarakunan shine’ fadar da suke zama ofisoshi ne na Shugabannin kananan hukumomi.Hukumar masu bautawa kasa bata iya ko kiran dalibai da suka kammala jami’oi, kai ba ma su iya tura wadanda suka kammala jami’a wadancan wuraren don aikin yi wa kasa hidima.

Sai yayi tambaya akan “Abinda ke faruwa ke nan yanzu? Ba haka bane Sarakunan sun dawo fadarsu hakanan ma Shugabannin kananan hukumomi sun koma ofisoshin su.Hukumar kula da al’amuran masu bautar kasa NYSC suna kiran wadanda suka kammala makarantu a ofisoshinsu na Jihohi, ana kuma tura su wadancan Jihohin.Ko yanzu za a iya cewa babu wani cigaban da aka samu.Don Allah mu bayyana gaskiya idan ita ce ta kasance ba wani boye- boye.”

Kan maganar maganar jiragen fadar Shugaban kasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fadi zai sayar da su ba lokacin da yake kamfen a shekarar 2015.

Hakanan ma Adesina yace Bishop na katolika Diocese ta Sakkwato Matthew Hassan-Kukah wanda ya bayyana cewa Shugaban kasa yayi alkawarin yin hakan kafin zaben shi.

Rahoton LEADERSHIP ya bayyana Kukah  bayanin sakon da yayi na Ista ta 2023 har ila yau ya sake yi ma Shugaban yarfe inda yace,”Yayin da kake shirin komawa Daura ko Kaduna,bana jin kai  a matsayinka kana ganin ka cimma duk wadansu kudurorin da kayi niyyar cimmawa,wato kamar kawo karshen ta’addanci tare da murkushe al’amarin rashawa,dawo da ‘yan mata,kai na kowa ne kamar yadda kake ba na kowa ba,sayar da Jiragen saman Shugaban kasa ka rika tafiya damu, dadaisauran wasu abubuwa.

Da yake maida martani kan suki- burutsun da Kukah ya yi Adesina ya ce shi mai wa’azin kirista ya cika sa siyasa a al’amuranshi domin duk wadansu hujjojinsa ya mamaye su da kalaman siyasa.

“Shi (Kukah) ya yi magana kan sayar da Jirginn Shugaban kasa,an taba yin wannan alkawarin?Kun san cewa a shekarar 2015,an bayyana wasu alkawura da aka yi da su ‘yan takarar basu sani ba.Don haka ta yaya zai fara soki- burutsun cewa yayi alkawarin hakan?”jami’aun al’amuran yada labarai na Shugaban kasa ya tambaya.

“Maganar sai da Jirgin Shugaban kasa kamata yayi shi (Kukah) ya bayyana alkawarin da Shugaban kasa yayi.Shugaban kasa yayi alkawari ne na zai duba yadda al’amarin yake ya kuma yi hakan an bada helikwabtoci ga sojojin sama sai kuma wasu helukwafta biyu zuwa uku da aka sayar,”.

Ya ce akwai maganar lura da kudaden da ake kashewa wajen lura da su helikwaftoci inda aka sayarda duk helikwaftocin abinda wasu basu amince da shi ba inda za a fara amfani da Nigerian Airways da har yanzun akwai shi.

Dangane da yaki da cin hanci da ta’addanci Adesina yace Buhari yayi kokarin shi a al’amarin tsaro da maganin rashawa,inda ya kara da cewa Nijeriya ba haka take ba a shekarar 2015 lokacin da Shugaban kasa ya hau kan karagar mulki.

“Shin muna kan al’amarin ta’addanci a shekarar 2015? ba’a ma kai ga gamawa da al’amarin gaba daya ba, amma ai ba muna inda muka samu kanmu ba?Idan Baba Kukah  zai yi ma kan shi adalci da kiran da yake yi, ya dace ya tuna da  cewa wannan kasa tamu Nijeriya ba haka take ba kamar  a shekarar 2015,”.

Buhari
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    2027:Yadda Kuɗi Da Siyasar Uban-gida Suka Daƙile Hanƙoron Matasa
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Rahotonni

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF
Rahotonni

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda 5 A Imo

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda 5 A Imo

LABARAI MASU NASABA

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.