• English
  • Business News
Saturday, July 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ina Rokon Allah Ya Sa Na Kammala Sana’ar Fim Cikin Mutunci – Jarumi Sadik

by Musa Muhammad
2 years ago
in Manyan Labarai, Nishadi
0
Ina Rokon Allah Ya Sa Na Kammala Sana’ar Fim Cikin Mutunci – Jarumi Sadik
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jarumi Sadik Muhammad Yalwa, wanda a ka fi sani da LUKMAN a cikin shirin kwana casa’in na tashar arewa 24, ya tattauna da wakilinmu, Musa Ishak Muhammad kan sana’arsa ta fim da yake yi inda suka tabo batutuwa daban-daban. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:

Da farko za mu so mu farawa da sanin cikakken sunanka da kuma takaitaccen tarihinka.

To Alhamdu lillah, da farko dai sunana Sadik Muhammad Yalwa, wanda a ka fi sani da Baba Sadik, jarumi a masana’antar Kannywood, fitacce a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango na tashar Arewa 24, wanda a ka fi sani a cikin shirin da Lukman dan Gwamna.

Takaitaccen tarihina kuma, ni haifaffen garin Gombe ne. A Gombe na yi karatun Firamare da na Sakandire. Daga bisani, na yi karatun addini a gurin mahaifina saboda mahaifina malamin addini ne. Daga nan kuma na dawo garin Jigawa inda na sake maimaita Sakandire a garin Hadeja. Sannan a nan Jigawar dai na je Polytechnic inda a nan na samu shedar (Diploma) a bangaren(Computer Science). Daga nan na kara zuwa makarantar( Informatics) a nan Kazaure. Daga nan ne na tafi Saint Monica International American Unibersity inda na je na yi karatun Digiri a fannin (Computer Science). Sannan na dawo gida Nijeriya na ci-gaba da gudanar da harkokina na karatu, kuma sannan ni dan kasuwa ne, kuma mai dokar hoto ne, kuma sannan jarumi ne.

Yaya aka yi ka samu kanka a cikin masana’antar Kannywood?

Labarai Masu Nasaba

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A ZaÉ“en 2027 Ba – NNPP

Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

E to, ni a gaskiya farko ban tashi da son yin fim ba, amma zama da ‘yan uwana irin su Usman Mu’azu wanda kowa ya san tsohon furodusa ne, da kuma kaninsa Yunusa Mu’azu, da kuma dan uwan Bilal Umar Baffa dukansu makusanta ne na harkar fina-finai, kuma ‘yan uwana ne na jini wadanda mu ke tare da su shekara da shekaru. To idan na zo wajensu a Kano ta dalilin haka na ke ganin jaruman Kannywood din da dama. To wata rana ina zaune sai kaninsu Yunusa Mu’azun wato Muhammad Mu’azu ya zo ya ce min Baba Sadik Arewa 24 suna neman jaruman Kwana Casa’in zango na biyu, saboda an yi zango na daya. To daga nan sai ya nuna mun ka’idojin da za a bi a nema. Cikin ikon Allah na nema, kuma a ka saka ranar tantancewa, muka je aka tantance mu a nan ofishin Arewa 24. Cikin ikon Allah. Wata rana kawai sai a ka kira ni a waya a ka ce, tantancewar da na zo na yi ta shirin Kwana Casa’in, Allah Ya nufa na samu. To daga nan sai na fara tuntubar iyayena domin neman amincewarsu. Mahaifina ya ce min ” Ba komai ai kai namiji ne kawai dai komai za ka yi ka ringa tuna inda ka fito kuma ka ringa tuna su waye iyayenka” to daga nan ne aka fara har kuma Allah Ya kawo mu matakin da a ke kai a yanzu.

Kasancewar a cikin shirin Kwana Casa’in ne ka fara fitowa a matsayin jarumi, yaya ka samu kanka a lokacin da ka fara aikin shirin?

To Alhamdu lillah gaskiya abu ne sabo a gurina, ban taba yi ba sai dai in gani a na yi. To gaskiya ranar da a ka fara saka min kyamar daukar hoto gaskiya na samu kalubale da yawa, na faduwar gaba da ido na mutane, wai an taru a na so ka yi abu, kuma wai a na so a ranka ka ji da gaske ake. Ga daraktoci ga kuma mutane a wajen a cike, gaskiya dai irin na dan ji tsoro, amma kuma da na ci-gaba da kokartawa, saboda kar na bawa wadanda su ka yarda zan iya kunya. To haka dai na yi ta kokari har Allah Ya sa na yi yadda ya kamata.

Tun a lokacin da ka je tantancewa ta shirin kwana casa’in, an shaida maka cewa a matsayin Lukman za ka fito, ko kuma sai da a ka fara aikin sannan a ka ce ga a abunda za ka fito?

E, lokacin da na je tantancewa na yi tantancewa ne a kan Lukman, amma ban san wa ne ne Lukman ba, kuma ban san me ne ne rawar da zai taka ba. Har sai da na je sa hannu a kwantiragi, to a nan aka bani sikirifit na karanta, sannan na ga ashe Lukman shi ne dan Gwamna, kuma kusan duka ragamar Zango na biyu na shirin yana da rawa mai yawa da zai taka a ciki.

Bayan shirin Kwana Casa’in, ka yi wasu fina-finai ne ko iya kwana casa’in kawai ka ke yi?

Eh gaskiya na yi wasu fina-finan bayan Kwana Casa’in na yi wasu fina-finan musamman masu dogon zango, amma dai gaskiya Kwana Casa’in shi ne jigo tunda a ciki a ka san ni. Amma daga baya na yi wasu fina-finan kamar su: Abu Nazir, Mudubina, Tsangayar Asali, Uku Sau Uku da dai sauran wasu da dama wanda na manta.

A cikin duka fina-finan da ka yi wane fim ne ya fi ka fi so kuma ya fi burge ka?

E to, a duka dai gaskiya Kwana Casa’in shi ne bakandamiya, domin sanadiyyar sa ne a ka sanni har a ke magana da ni, saboda haka duk wata nasara da na samu ta sanadiyyar sa ne. To mai bi masa kuma shi ne fim din Abu Nazir, da kuma sauran duka fina-finan da na yi ina son su.

A cikin duka wadannan fina-finan da ka yi mene ne abin da ya fi faranta maka rai wanda ka yin farin ciki a duk sanda ka tuna?

E to, Alhamdu lillah gaskiya abu na farin ciki da ba zan iya mantawa da shi ba, shi ne kasancewar da mutane a sansanin daukar shirin Kwana Casa’in a Jigawa. A lokacin akwai irin su Saminu Baba, Abba S Boy, Sahabi Madugu, da su Abdul `ya`yan Gwamna Bawa Mai Kada da dai sauransu. To gaskiya mun yi zama mai dadi wanda kullum na tuna ya na saka ni farinciki gaskiya.

Mafi yawan lokuta idan a ka samu farin ciki a na iya samun akasinsa, me za ka iya tunawa wanda ya ke bata maka rai a duk sanda ka tuna?

To haka ne gaskiya kusan duk inda a ka samu farin ciki to a kan iya samun akasinsa, to amma ni gaskiya farin ciki nake rikewa ba na iya rike bakin ciki. Koda raina ya baci nakan yi kokari a lokacin kawai na manta. To wallahi ni yanzu ba zan iya tuna ma wani abu na bakinciki da na ke iya tunawa ba, saboda ni ba na barin bakinciki a cikin raina. Saboda haka ba zan iya tuna wani abu da ya ke bata min rai ba.

A cikin jerin jaruman da ka yi aiki da su maza da mata wadanne jarumai ne ka fi jin dadin aiki da su?

To gaskiya dai jarumi wanda a ka fi ganin mu tare da shi shi ne Abba John da kuma Saminu Baba, sai kuma Rayya a mata, duka ina jin dadin aiki da su sosai, saboda mafi yawan fitowar da na yi da su ne a cikin shirin Kwana Casa’in. Da ire-iren su dai da yawa.

Mene ne burinka a cikin wannan masana’anta ta kannywood?

Dariya, to buri dai shi ne Allah ya sa yadda muka fara wannan sana’a lafiya, Allah Ya sa mu gama ta lafiya. Allah kuma Ya sa kar mu hadu da wani abu da zai jawo mana zubewar mutunci. Ni kullum burina shi ne, Allah Ya sa yadda na shiga masana’antar fina-finai lafiya, Allah Ya sa na gama lafiya tare da mutuncina da na sauran ‘yan uwa baki daya.

Shin kana da aure kuwa kuma wanne irin nau’in abinci ne ya fi burge ka?

Gaskiya ba ni da aure sai dai niyya. Abinci kuma duk wanda ya zo gabana a lokacin da na ke jin yunwa to shi ne wanda na fi so a wannan lokaci.

A karshe mene ne sakonka na karshe ga masoyanka masu bibiyar fina-finanka?

Masoya mu na yi musu fatan alkhairi kamar yadda su ke yi mana a koda yaushe, kuma in sha Allah za mu ci-gaba da zuwar musu da abunda ya dace da al’adun Hausawa da kuma fadakarwa da nishadantarwa inshaAllahu.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: FimJarumiKannywoodSadik
ShareTweetSendShare
Previous Post

Fasahar Sadarwa Ta GPRS

Next Post

Ta Ya Za A Magance Rashin Tsaftar Yara Mata Masu Tasowa?

Related

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A ZaÉ“en 2027 Ba – NNPP
Manyan Labarai

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A ZaÉ“en 2027 Ba – NNPP

5 hours ago
Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Manyan Labarai

Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

9 hours ago
‘Yansanda Sun Kama Barayi 15, Sun Kwato Motocin Sata 20 A Kano
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja

1 day ago
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Manyan Labarai

Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha

1 day ago
Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace
Manyan Labarai

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

1 day ago
‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi

1 day ago
Next Post
Ta Ya Za A Magance Rashin Tsaftar Yara Mata Masu Tasowa?

Ta Ya Za A Magance Rashin Tsaftar Yara Mata Masu Tasowa?

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

July 5, 2025
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

July 5, 2025
Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

July 5, 2025
Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

July 5, 2025
Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (5)

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (5)

July 5, 2025
ALGON Ta Taya Gwamnan Sani Murnar Samun Lambar Yabo Ta Kasa

ALGON Ta Taya Gwamnan Sani Murnar Samun Lambar Yabo Ta Kasa

July 5, 2025
Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A ZaÉ“en 2027 Ba – NNPP

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A ZaÉ“en 2027 Ba – NNPP

July 5, 2025
Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu

July 5, 2025
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8)

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8)

July 5, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

An Kama Matashin Da Ya Yi Garkuwa Da Abokinsa Tare Da Karbar Kudin Fansa

July 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.