Shafin Adabi na wannan makon, na tafe da fasihiyar marubuciya, hazika, gwarzuwar da ta yi nasarar lashe gasar HIKAYATA ta BBC HAUSA a shekara 2023 da ta gabata. AISHA SANI ABDULLAHI wacce aka fi sani da DAYYEESHATUL HUMAIRA, ta bayyana wa masu karatu yadda ta tsinci kanta a fannin rubutu tare da irin gwagwarmayar da ta sha kafin ta fara rubutu har ma da yadda rubutun ya kasance, tare da wasu batutuwan da suka shafi rubutunta. Ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU kamar haka:
Ya sunan Malamar?
Sunana Aisha Sani Abdullahi Wacce a duniyar marubuta da makaranta aka fi sani da Dayyeesherthul-humaerath.
Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinki.
Ni haifaffiyar Jihar Filato ce, karamar hukumar Jos ta Arewa, na yi karatun firamare da Sakandire a ‘Maria Memorial college’ da ke cikin garin Jos, yanzu haka na samu gurbin karatu ina daf da farawa, ni marubuciya ce kuma ‘yar kasuwa, kazalika ni budurwa ce.
Me ya ja hankalinki ki ka tsunduma cikin rubutu?
A da, ina rubutu ne kawai don ra’ayina, amman a yanzu ina rubutu ne da ra’ayin kawo gyara ga rayuwar al’umma har ma da ni karan kaina.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
An sha fama, domin na so yin rubutu ba tare da na iya karatun ba ma bare in kai ga rubutawar. Kasancewar garin Jos ba gari bane na hausa ba a koyar da ita har sai an je matakin sakandare. Kuma anan dinma kutsawa cikinta kawai ake ba daga farko ba. Ni kuma tun ina ajin farko js1 kenan nake kudurta yin rubutu har ya kai ga bana kashe kudin Break dina ina siyan ‘note book’ don in yi rubutu, bana iyawa kuma bana fasa siyan koda na bata, a karshe dai wani malamin na hausa muna aji hudu, ss1 ya ce dole sai mun rubuta labari wanda shi ne CA dinmu mun dauka wasa mun shirmantar da abun da tunanin ba za mu iya ba, sai da muka ga ya dage yana kan bakarsa na batun CA kafin muka yi. Wanda shi ne littafina na farko da na yi masa take da SO SARKI NE. Daga nan ban kara waiwayar rubutu ba kusan shekara guda tukun na hadu da wata marubuciya kawata, ni ina rubuta wasan kwaikwayo a Facebook group ita kuma tana nobel kamar wasa muna magana ta ce ai in gwada duk abu daya ne zan iya, na nuna mata cewa ba zan iya ba, ta ce zan iya, daga nan dai na fara rubutu online.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara rubutu?
Tsakanin 2016/17 na fara rubutu.
Kin rubuta Labari sun kai kamar guda nawa?
Na rubuta labarai kusan sha bakwai, ban da gajeru zallan cikakkun nobel ne 17. Gajeru ba na ce ga yawansu ba.
Wanne labari ne ya zamo bakandamiyarki cikin wadanda ki ka rubuta?
Duk ina son littafaina kuma kowanne bakandamiyata ne, amman zan iya cewa SAI NA AURI MARUBUCI na daban ne kasancewar hargagin da kawo cikin marubuta har ma da makarantan.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu kina sha’awar fara rubutu shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Gaskiya ba a san ina rubutu ba a gida, sai da na kwashe shekaru ma kafin mahaifiyata da yayata suka sani, kuma su din gaskiya ban fuskanci wani kalubale gare su ba, sai kuma cin gasar hikayata da ya fasa kowa ma ya sani.
Cikin labarun da ki ka rubuta ko akwai wanda ki ka buga?
Na buga SAI NA AURI MARUBUCI kuma ina da kudirin buga wasu ma In sha Allah.
Wanne irin kalubale ki ka fuskanta game da rubutu?
Kalubale akan littafin SAI NA AURI MARUBUCI inda aka kai ruwa aka kai gari wanda abun da ke bani mamaki shi ne harda Marubuta ciki.
Wanne irin nasara ki ka samu game da rubutu?
Ba adadi, in na ce ba adadi ina nufin ba za a iya misaltasu ba, kullum cikin kara samun nasara nake a rubutu daga ranar dana fara har kawo yanzu kuma yau da nake yi miki magana.
Kamar wanne bangare kika fi maida hankali a kai wajen yin rubutu?
Labaran abubuwan da na san ba a fiye maida hankali kai ba, kuma suka kasance masu mahimmanci ga rayuwar al’umma gabadaya.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Rubutuna ya zam bango abin jingina ga rayuwar Sani, wannan shi ne burina.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka game da rubutu?
Duniyar rubutu ai dole akwai abu biyu yabo da akasinsa, kowanne muna samu kuma muna godiya tare da nuna jin dadin cewa mun kai munzalin da za mu yi rubutu har ya kai ga an magantu kai.
Me ya fi saurin saka ki farin ciki?
Na kan ji dadi in na tuna cewa na rubuta abun da zai amfanar da rayuwar al’umma.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
A yanzu na dauki rubutu tamkar wani bangare ne na rayuwata, ban jin cewa zan iya barinsa sai ranar da numfashi ya bar jikina.
Bayan rubutu kin ce kina sana’a, kamar me ki ke siyarwa?
E! Ina saida jewelries.
Ya ki ke iya hada sana’arki da kuma rubutunki?
Kowa da lokacinsa na kan ware lokaci domin yin rubutu ko in ya kasance ina zaune ba abun da nake.
Kamar wanne lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Lokacin da ba hayaniya, na zauna ni kadai ya fi mun dadi gaskiya.
Me za ki ce ga masu karanta labaranki?
Allah ya yi masu albarka,
ya biya masu bukatunsu na Alkairi duniya da lahira, kuma ya sa su amfana ga dukkan abun da suka karanta.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Mahaifiyata, Mahaifina, Yan Uwana, Marubuta. Makaranta, duk na gaida ku.