Hukumar ZaÉ“e Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta amince da David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC.Â
Wannan ya biyo bayan sake sauya shugabancin jam’iyyar kafin zaɓen 2027.
- Sin Za Ta Kafa Yankin Kare Muhallin Halittu Na Huangyan Dao
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria
David Mark yanzu shi ne shugaban riÆ™on Æ™warya, yayin da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, ya zama Sakataren jam’iyyar na Ƙasa.
Wasu manyan mutane da suka haɗa da tsohon gwamnan Edo, Oserheimen Osunbor, a matsayin Lauyanta na Ƙasa; Ibrahim Mani a matsayin Ma’aji; da Akibu Dalhatu a matsayin Sakataren Kuɗi.
‘Yan adawa sun zaÉ“i jam’iyyar ADC a matsayin dandamalin siyasa a ranar 2 ga watan Yuli, 2025, domin fafatawa a zaÉ“en shugaban Æ™asa da sauran zaÉ“uka na 2027.
Mark ya ce haÉ—akarsu na da burin “ceto Nujeriya, gina dimokuraÉ—iyya”.
Manyan ‘yan siyasa a haɗakar sun haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, Dino Melaye, Solomon Dalong.
Sauran sun haÉ—a da Dele Momodu, Gabriel Suswam, Ireti Kingibe, Emeka Ihedioha, da Air Marshal Sadique Abubakar (ritaya).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp