ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Ta Buƙaci Majalisa Ta kirkiro Dokar Hana ‘Yan Siyasa Zuwa Rumfunan Zabe Da Maƙudan Kuɗaɗe

by Yusuf Shuaibu
10 months ago
Inec

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi kira ga majalisar dokokin ƙasar nan da ta samar da tsauraran dokoki da ke haramta wa ‘yan siyasa zuwa da maƙudan kuɗaɗe a rumfunan zaɓe domin daƙile saye da sayar da ƙuri’u da sauran kura-kurai a lokacin zaɓe.

Wannan kuma na zuwa ne daidai da lokacin da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zabe, Hon. Adebayo Balogun ya sanar da shirin kafa dokar zabe ta 2025 domin maye gurbin na 2022 da ake yi a yanzu, wanda ya ce ya fallasa gibi a zaben 2023.

  • Da Yiwuwar Wasu Gwamnoni 5 Su Sauya Sheka Kafin Zaben 2027
  • INEC Ta Goge Sunayen Matattu 7,746 Daga Rajistar Zabe

Da yake jawabi a wajen wani taron tuntuba da jami’an tsaro da kwamitin kwararru kan gyaran dokokin zabe a Abuja ranar Juma’a, Daraktan INEC, Tanimu Muhammed, ya bayyana yadda ake kara nuna damuwa kan sayen kuri’u, wanda ya zama babbar barazana ga tsarin dimokuradiyyar Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Taron wanda kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan harkokin zabe suka shirya tare da hadin gwiwar Cibiyar Bayar da Shawara ta Siyasa (PLAC) da goyon bayan Ofishin Harkokin Wajen Ingila, da kungiyar kasahen rainon Ingila da Ofishin Ci Gaba na Burtaniya (FCDO), ya samar da wani dandali ga masu ruwa da tsaki don tattauna batun tsaro da sauye-sauyen doka.

Wakilin INEC ya lura da cewa ‘yan siyasa kan bayar da hujjar daukar makudan kudade a ranar zabe ta hanyar ba da misali da kudaden da wakilan jam’iyyar ke kashewa da kuma wasu bukatoci. Sai dai kuma ya yi gargadin cewa rashin takaita yawan kudaden da ake zuwa rumfunan zabe da su ya kara rura wutar siyan kuri’u da kuma kawo cikas ga ingancin zabe.

LABARAI MASU NASABA

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

Domin magance wannan kalubale, Muhammed ya ba da shawarar ka da a bar mutane su dauki kudi fiye da naira 50,000 a rumfunan zabe.

“Sayen kuri’u na daya daga cikin manyan barazana ga sahihin zabe a Nijeriya. Muna bukatar dokar da ba wai kawai ta haramta wannan dabi’ar ba har ma da sanya matakan kariya,” in ji Muhammed.

Bayan sayen kuri’u, jami’an INEC sun sake jaddada bukatar da suka dade suna yi na a kafa hukumar da ke yaki da laifukan zabe, suna masu cewa hukumar zabe ba ta da karfin gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

A cewar Muhammed, “INEC na iya bakin kokarinta wajen ganin an gurfanar da masu laifukan zabe a gaban kotu, amma muna bukatar wata cibiya mai kwazo da ke da hurumin shari’a da kayan aiki domin gudanar da bincike tare da hukunta masu aikata laifukan zabe. Samar da hukumar zai tabbatar da cewa hukuncin sayen kuri’u, satar kuri’u, da sauran laifuffuka cikin gaggawa”.

Kwamishinan ‘yansanda mai kula da tsare-tsare da tantance harkokin zabe, Abayomi Shogunle, wanda ya wakilci babban sufetan ‘yansanda, ya yi nuni da cewa rashin isassun kayan aiki ya kan kawo cikas ga kokarin tabbatar da doka a lokacin zabe. “Muna fuskantar manyan kalubalen kayan aiki, tun daga tura jami’ai zuwa lunguna da sako da kuma tabbatar da sadarwa a lokacin zabe. Wadannan batutuwa ne da ya kamata a magance su idan ana son a aiwatar da dokokin zabe yadda ya kamata,” in ji Shogunle.

Da yake mayar da martani kan matsalolin da suka taso, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zabe, Hon. Adebayo Balogun, ya bayar da tabbacin cewa za a magance dukkan batutuwan da aka tattauna tare da sake fasalin zabe a nan gaba.

“Dokar zaben 2022, tana da matukar muhimmin wajen ci gaba, amma aiwatar da ita a babban zaben da ya gabata ya nuna wuraren da ke bukatar gyara. Mun himmatu wajen karfafa dokokin zabenmu don nuna gaskiyar dimokuradiyyarmu,” in ji Balogun.

Ya jaddada cewa, baya ga garambawul na majalisar, akwai bukatar kara wayar da kan jam’iyyun siyasa, jami’an INEC, da kungiyoyin fararen hula kan illolin da ke tattare da sayen kuri’u da sauran kura-kurai a zaɓen ƙasar nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Siyasa

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

December 18, 2025
Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe
Siyasa

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

December 16, 2025
El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
Siyasa

El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027

December 15, 2025
Next Post
Kayan Abinci: Gwamnatin Nijeriya Ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Rage Farashi

Kayan Abinci: Gwamnatin Nijeriya Ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Rage Farashi

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.