Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya bukaci a samar da tsaro a dukkanin yankunan da za gudanar da zaben cike gurbi a kasar nan.
Yakubu ya yi wannan kiran ne a lokacin wata ganawa da kwamitin samar da tsaro kan zabe a Abuja.
- Tsadar Magunguna Na Barazana Ga Rayukan Majinyata A Nijeriya
- Gwamatin Tarayya Ta Fito Da Tsarin Cin Gajiyar Ma’adanan da Ke Jihar Nasarawa
Ya bayyana cewa akwai zaben da za a yi a watan Fabrairu har kashi biyu, na farko shi ne, zaben cike gurbi wanda aka samu sakamakon mutuwa ko ajiye aiki ga ‘yan majalisun tarayya da na jiha, inda a zaben zai guda a mazabar ‘yan majalisar dattawa guda biyu da kuma ‘yan majalisar wakilai a jihohi uku. Sannan ya ce zaben kashi na biyu kuma za a gudanar da shi ne sakamakon hukuncin kotu.
Idan za a iya tunawa an gudanar da ire-iren wannan ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a watan da ya gabata, shugaban INEC ya ce a baya an shirya za a gudanar da zaben cike gibi ne a mazabu 35 da ke fadin kasar nan.
Sai dai ya ce a yanzu haka an samu karin mazabu hudu wanda kotun daukaka kara ta umurci hukumar ta gudanar da zabe a mazabar Yabe/Shagari da ke Jihar Sakwato da Madara/Chiade a Jihar Bauchi da kuma Kudan da Kauru/Chawai na Jihar Kaduna.
“Da wannan ne aka samu jimillar mazabu 39 za a gudanar da zaben cike gibi a fadin kasar nan baki daya. Daga cikin adadin, mazabu 9 za a gudanar da sabon zabe ne.
“In ban da guda uku daga cikin mazabun da suka hada da Filato ta Arewa da Arewacin Jos/Bassa a Jihar Filato da Kachia/Kagarko a Jihar Kaduna, duk sauran zaben zai gudana ne a akwatunan zabe kalilan. A wasu wuraren kuma, akwatin zabe guda daya ne kawai za a gudanar da zaben.
“Babban aikin kwamitin samar da tsaro shi ne, tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana. Bisa wannan dalilin ne, hukunar ta riga ta sanar da cewa rundunar ‘yansandar Nijeriya ce za ta jagoranci al’amuran tsaro a lokacin zabe a dukkanin mazabu da ke fadin kasar nan.
“Mun fitar da adadin yawan masu kada kuri’a da suka amshi katin zabe a dukkanin rumfunan zabe da ke fadin kasar nan.
“Duka bayanan da muka yi a baya su ne muka sake maimaitawa a wannan ganawa da mambobin kwamitin samar da tsaro. Sannan za mu saka dukkan bayanan a shafukan sada zumanta na hukumarmu bayan wannan ganawa saboda fadakar da mutane.
“A matsayinmu na hukumomin tsaro, hakkinku ne ku tsare yankunan da za a gudanar da zaben domin ba mu damar jibge jami’anmu da kayayyakin zabe da tsare masu saka ido ciki har ma da ‘yan jarida da wakilan jam’iyyu da kuma ‘yan takara. Idan har ba a samu tsaro ba a mazabun, ba za mu iya gudanar da sahihin zabe ba.
“Bisa abubuwan da suka gabata a baya, zaben cike gurbi yana da matsaloli masu tarin yawa. Za mu mayar da hankali wajen rage lamarin a bangaren wasu ‘yan takara da kuma magoya bayansu.”