Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta dakatar da sake gudanar da zabubbukan cike gurbi da aka gudanar a wasu mazabu na jihohin Enugu, Kano, da Akwa Ibom, sakamakon tarzoma, da rashin bin ka’ida, da kuma sace jami’an zabe.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da mazabar Enugu ta Kudu 1 a jihar Enugu, da kuma mazabar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, da kuma mazabar Kunchi/Tsanyawa da ke jihar Kano.
- Kamfani Zai Inganta Harkokin Harkar Ma’adanai Ta Hanyar Fasaha
- Kakakin Majalisa Ga Tinubu: Ka Dauki Kwararan Matakai Kan Karuwar Matsalolin Tsaro
Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Sam Olumekun, a ranar Asabar.
Dakatarwar ta biyo bayan rahotannin cewa, an ga gungun ‘yan daba da ke kawo cikas a wani wuri da sace kayan zabe a wadannan jihohinn.
A mazabar Kunchi/Tsanyawa da ke jihar Kano, an dakatar da zabuka a dukkanin mazabu goma da ke karamar hukumar Kunchi sakamakon muggan ayyukan ‘yan daba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp