Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta fara raba muhimman kayayyakin aikin gudanar da zabe a Jihar Adamawa.
Raba kayayyakin na daga cikin shirye-shiryen gudanar da babban zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar.
- An Daure Dan Kamasho Wata 6 Kan Satar Batirin Mota A Abuja
- Sojojin Sin Suna Da Kwarin Gwiwa Wajen Aiwatar Da Ayyukan Tabbatar Da Tsaro A Duniya
Da yake magana lokacin raba kayan a harabar Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke Yola, shugaban hukumar zaben jihar, Barista Hudu Yunusa, ya ba da tabbacin kayan aikin zaben zai isa cibiyoyin kada kuri’a kafin ranar gudanar da zaben.
Haka kuma shugaban hukumar, ya ce hukumar ta raba kayayyakin ne a kan idon jami’an tsaro da jam’iyyu, lamarin da ke nuni da hukumar za ta gudanar da sahihin zabe.
Shugaba, ya kuma yi kira ga jam’iyyu da ‘yan takara da su hada hannu wajen tabbatar da lamura sun tafi daidai lokacin gudanar da zaben.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kayayyakin zaben da wuraren gudanar da zaben ke nisa da Yola fadar jihar, ko rashin kyawun hanyoyi da INEC ta fara rabawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp