Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da abin da ake kira “balan balan leken asiri” na kasar Sin a wani taron manema labaru da aka shirya Alhamis din nan. Yana mai cewa, yana adawa da kalaman rashin gaskiya da wasu mutane ke furtawa a Amurka, tare da fatali da gaskiyar lamari. Ya ce, tarihi ya tabbatar kuma zai ci gaba da tabbatar da cewa, a ko da yaushe sojojin kasar Sin sun kasance masu tsayin daka wajen aiwatar da ayyukan tabbatar da tsaro a duniya, da yin hidimar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bli-Adama.
Ya kara da cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana tsayawa kan manufar kasancewa wadda ba za ta taba fara amfani da makaman nukiliya a kowane lokaci, a kowane hali, kuma ta yi alkawarin ba za ta yi amfani da makaman nukiliya ba, ko kuma ta yi barazanar yin amfani da makaman nukiliya a kan kasashen da ba su da makamin nukiliya, da kuma yin barazanar yin amfani da makaman nukiliya kan yankunan da ba su da makamin nukiliya. (Mai fassarawa: Ibrahim)